Shugaban Turkiyya Erdoga ya jaddada kira ga MDD ta sanya wa Isra'ila takunkumin makamai

Shugaban Turkiyya Erdoga ya jaddada kira ga MDD ta sanya wa Isra'ila takunkumin makamai

Shugaban Turkiyya ya yi gargaɗin cewa duk ranar da ta wuce ba tare da tsagaita wuta ba to tana matso da yaƙi ne zuwa yankin.
A yayin taron, an tattauna hanyoyin da za a bi a samu zaman lafiya mai dorewa a ƙasashen da suka yi haɗaka na ƙungiyar. / Hoto: AA

"Takunkumin Majalisar Ɗinkin Duniya zai zama wani mataki mai tasiri na tsayar da ita," a cewar Shugaban Turkiyya Tayyip Erdogan, yana mai shan alwashin cewa Turkiyya za ta ci gaba da neman a ɗauki wannan mataki "a duk inda ya samu kansa."

A ranar Juma'a Erdogan ya yi gargaɗin cewa idan dai ba a tsagaita wuta ba, to kowace rana tana ƙara kusanto da yaƙi ne a yankin. Ya bayyana cewa Isra'ila tana so ta ringa tunzura ƙasashe don ta faɗaɗa yaƙin.

Shugaba Erdogan, tare da Minista Fidan sun karɓi ministocin harkokin waje daga Azerbaijan da Armenia da Iran da and Rasha a Istanbul, a wani ɓangare na taron haɗin kai da aka kira South Caucasus Regional Cooperation Platform, a Turancin Inglishi.

Yayin taron a Fadar Shugaban Ƙasa ta Dolmabahce, Erdogan ya jaddada aniyar Turkiyya ga haɗakar ƙasashen, da ke da manufar warware matsalolin yankin ta hanyar tattaunawa

A yayin taron, an tattauna hanyoyin da za a bi a samu zaman lafiya mai dorewa a ƙasashen da suka yi haɗaka na ƙungiyar.

Shugaba Erdogan ya jaddada aniyar Turkiyya ga haɗakar wajen warware batutuwan da suka shafi yankin ta hanyar tattaunawa.

Ya kuma bayyana gamsuwa da ci gaban da yankin yake samu wajen dawwamammen zaman lafiya, sannan ya yi alƙawarin ci gaba da goyon bayan yunƙurin zaman lafiya tsakanin Azrbijan da Armenia.

"Yadda haɗakar ƙasashen take wajen ci gaba da samun lafiya mai ɗorwa abin ƙarfafa gwiwa ne," a cewar Erdogan. Ya ƙara da cewa goyan bayan haɗakar za ta ƙara nuna tasirin tattaunawa a matsayin hanyar samun zaman lafiya.

TRT World