Shugaban Falasdinawa Abbas na jawabi ga majalisar dokokin Turkiyya a Ankara/ Hoto: Reuters

A ziyarar da ya kai Turkiyya a wani muhimmin lokaci, shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya yi jawabi a gaban majalisar dokokin Turkiyya a wani zama na musamman da aka yi, wanda aka kira domin nuna goyon baya ga fafutukar Falasdinu.

Da yake ƙarin haske kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa yankunan Falasdinawa, musamman Gaza, Abbas a ranar Alhamis ya jaddada cewa "Falasdinawa sun tsaya ƙyam wajen adawa da masu tsananin kishin kafa ƙasar Falasɗinu da ke neman mamaye yankin baki daya."

Abbas ya kuma ce Falasdinu ta yi matuƙar godiya ga kakkausan matakin da Turkiyya ta ɗauka na ƙin amincewa da yin Allah wadai da "yaƙin kisan ƙare dangi da Isra'ila ke yi kan Falasdinawa."

Ya kara da cewa, "Muna kira ga dukkan jama'a da su tsaya tare da mu wajen 'yantar da fursunonin Falasdinawan sama da 10,000 da ke tsare a gidajen yarin Isra'ila," yana mai kira ga ƙasashen duniya da su dauki matakin gaggawa da inganci wajen tsagaita wuta ta dindindin.

Abbas ya ci gaba da jaddada cewa, "Gaza da Gabashin Kudus, da Yammacin Gabar Kogin Jordan, yanki ne guda daya da ya kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta bisa dokokin kasa da kasa."

Zargin kisan ƙare dangi

Isra'ila ta fuskanci Allah wadai daga ƙasashen duniya saboda yin watsi da ƙudirin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya buƙaci a tsagaita wuta cikin gaggawa.

Sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa sama da 40,000 a Gaza, yawancinsu mata da kananan yara, a cewar hukumomin lafiya na Falasdinu.

Fiye da watanni goma a cikin yakin Isra'ila, yankunan Gaza da yawa sun zama kufai kuma sun kasance a cikin ƙawanyar hana shigar musu da abinci da ruwa mai tsabta, da magunguna.

Ana zargin Isra'ila da kisan kiyashi a kotun kasa da kasa, wacce a hukuncinta na baya-bayan nan ta umarci Tel Aviv da ta gaggauta dakatar da kai hare-hare a kudancin birnin Rafah, inda Falasdinawa sama da miliyan daya suka nemi mafaka.

TRT World