Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi bikin cika shekaru 571 da ƙwace birnin Istanbul, wani muhimmin lamari a tarihin Turkiyya da na duniya, a cewar Hukumar Sadarwa ta Turkiyya.
"Ina murnar cika shekaru 571 da mamayar Istanbul, daya daga cikin manyan nasarori a tarihin duniya da tarihinmu," in ji Erdogan a ranar Laraba, yana mai jaddada muhimmancin wannan nasara mai cike da tarihi.
Har ila yau, Hukumar Sadarwa ta Turkiyya ta bayyana a shafin X cewa Shugaba Erdogan ya jaddada mahimmancin "fahimtar ruhi" da kuma muhallin cin nasara.
Ya yi nuni da irin hazakar soji da azama da juriya, wanda ke nuna irin kokarin da sojojin Daular Usmaniyya suka yi, karkashin jagorancin Fatih Sultan Mehmet sarki na bakwai na Daular Usmaniyya, wanda ya fara mulki daga shekarar 1444 zuwa 1446 sannan daga shekarar 1451 har zuwa rasuwarsa a shekara ta 1481.
Erdogan ya kara da cewa, wannan nasara ba wai kawai ta taimaka wajen yaduwar Daular Usmaniyya ba ne, har ma ta kafa Istanbul a matsayin wata cibiyar "dunkulewar al'adu da addinai" daban-daban, saboda salon mulkin Sultan Mehmet na "haƙuri da adalci".
Zuwa 'karnin Turkiyya'
Shugaban ya nuna kamanceceniya tsakanin "ƙuduri" na zamanin Sultan Mehmet da kuma burikan zamani, yana mai nuni da cewa irin wannan ruhi na "juriya da imani" ne ke jagorantar Turkiyya zuwa ga manufofinta na gaba, musamman na "ƙarnin Turkiyya."
Erdogan ya kammala sakon nasa da jinjina ga wadanda suka yi nasarar mamaye birnin yana mai cewa: “A daidai lokacin da ake cika shekaru 571 da samun nasarar mamaye birnin Istanbul, ina tunawa da rahama da girmamawa da godiyar Fatih Sultan Mehmet tare da shahidanmu da suka tafi. mu wannan birni mai kyau na duniya wanda babu irinsa, kuma ina mika gaisuwata ga dukkan 'yan kasarmu."
Mamayar birnin Istanbul, wanda ake kuma kira da "Fall of Constantinople," wato Faduwar Konstantinoful, ya faru ne a ranar 29 ga Mayun 1453, kuma ya nuna wani muhimmin sauyi a tarihin duniya.
Wannan lamari ya haifar da rugujewar Daular Rumawa da kuma hawan Daular Usmaniyya a matsayin babbar mai iko.