Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya amsa tambayoyin ƴn jarida a yayin da yake cikin jirgi a hanyarsa ta dawowa daga Girka bayan kammala Babban Taron Kan Hadin Kai tsakanin Turkiyya da Girka, kjaro na biyar.
Shugaba Erdogan a ranar Alhamis ya ce ya yi amannar cewa za a shiga sabon zamani na dangantaka tsakanin Turkiyya da Girka bayan ziyarar da ya kai Athens, wacce ta kasance mai tagomashi.
"Turkiyya da Girka sun samu isasshen ilimi da jajircewa wajen warware matsalolinsu ba tare da wani ya shiga tsakani ba," ya ce.
Ya ƙara da cewa, ƙasashen biyu sun tattauna kan dangantakar da ke tsakaninsu da ta haɗa da kasuwanci da yawon buɗe ido da batun Bahar Rum da mai yiwuwa haɗin kai kan makamashi da kuma yanayin da ake ciki a yankin Gaza na Falasɗinu.
Yayin ziyarar tasa, shugaban na Turkiyya ya gana da Shugaban Ƙasar Girka Katerina Sakellaropoulou da kuma Firaministan Girka Kyriakos Mitsotakis a Atina.
Gabashin Bahar Rum
A kan maganar rikicin makamashi na Gabashin Bahar Rum, Shugaba Erdogan ya jaddada yiwuwar shigar da dukkan ƙasashen yankin cikin lamarin bisa adalci.
"Ba ma yin katsalandan a cikin ƴncin kowa, za mu jajirce wajen ganin ba a keta mana ƴancinmu ba a Gabashin Bahar Rum, da tabbatar da cewa an yi rabo na adalci," ya ce.
Ya kuma ba da shawarar faɗaɗa haɗin kan ta wajen sanya batun makamashin nukiliya da kuma fitar da makamashin zuwa ƙasashen waje, wanda aka gina cibiyarsa a arewacin gundumar Turkiyya.
"Tashe-tashen hankulan da ake samu a Gabashin Bahar Rum yana mummunan tasiri a kan Turkiyya da Girka, ƙasashe biyu masu muhimmanci a yankin," in ji Shugaba Erdogan.
Ya jaddada cewa akwai buƙatar ƙasashen biyu su nemi damarmakin da za su amfani ƙasashensu duk da ƙalubalen da ake fuskanta a yankin.
Kasar Isra'ila ta ta'addanci
A kan batun Gaza, ya jaddada imaninsa cewa Falasɗinu ce za ta yi nasara, wanda hakan ke nufin nasara ce ta zaman lafiya a duniya da farfaɗo da tabbatar da ƴancin ɗan'adam.
Ya kara da cewa, "Ya zama dole (Firaiministan Isra'ila) Netanyahu da abokan aikinsa, su fuskanci hukunci mai tsauri da zai zama abin buga misali ga duk wadanda suka aikata kisan kiyashi," in ji shi.
Da yake tsokaci kan ta'addancin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila, ya ce, "Ina kasashen Yamma, Amurka? Gaskiyar ta tabbata, an kashe fiye da 17,000, ta yaya za mu lamunci hakan?"
Ya ce ya gaya wa Firaiministan Girka Mitsotakis cewa "Da mun so ganin Girka tana goyon bayan Falasdinu (a ƙuri'ar MDD); da ma ba ƙu kaurace wa zaben ba."
Yarjejeniyar Azerbaijan-Armenia
Dangane da kasar Faransa da ke bai wa Armeniya motocin sulke, shugaban na Turkiyya ya ce "Wannan tsokana ce, ya kamata Faransa ta san ba su yi wa Armeniya alheri ba amma suna aikata ba daidai ba."
Kasashe biyu, Azabaijan da Armeniya sun sanar a cikin wata sanarwa da yammacin jiya Alhamis cewa, sun amince da sakin fursunonin a wani mataki na samar da zaman lafiya.
Ya sake nanata cewa "Zai kasance fi alheri ga Armeniya a yi amfani da damar samun zaman lafiya, ka da a fada tarkon batattun kasashe."