Shugaba Erdogan ya gana da takwaransa na Masar El Sisi da Yariman Saudiyya bin Salman

Shugaba Erdogan ya gana da takwaransa na Masar El Sisi da Yariman Saudiyya bin Salman

Shugaban Turkiyya ya tattauna da shugabannin duniya da dama a Indiya yayin da ake taron G20.
Ana sa ran Shugaba Erdogan zai ci gaba da tattaunawa da wasu shugabannin duniya kafin a kammala taron. Hoto/Reuters

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gana da takwaransa na Masar Abdel Fattah el Sisi da Yariman Saudiyya mai jiran gado Mohammed bin Salman a Indiya.

Tattaunawar wadda suka yi kofa a garkame, an yi ta ne a yayin da ake taron G20 wanda ake yi a New Delhi.

A lokacin da aka soma taron a rana ta biyu, Firaiministan Indiya Narendra Modi ya yi maraba da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da sauran shugabannin kasashe a Rajghat.

Shugabannin G20 sun kai ziyara wurin tunawa da jagoran neman ‘yancin na Indiya Mahatma Gandhi a ranar Lahadi, kwana guda bayan kungiyar ta G20 ta kara samun sabuwar mamba da kuma cimma matsaya kan matsaloli daban-daban, sai dai sun sassauta magana kan batun yakin Rasha da Ukraine.

Sun dora furanni a wurin da kabarin Mahatma Gandhi yake kafin suka zarce wurin taron shuka itatuwa.

Za a yi taro na uku kuma na karshe na G20 mai taken “makoma daya” a sabon dakin taron da aka kaddamar na Bharat Mandapam inda aka yi gunkin Nataraja.

Shugaban Turkiyya Erdogan zai ci gaba da tattaunawa ta rufe kofa da wasu daga cikin shugabannin kasashen duniya kuma ana sa ran zai tattauna da ‘yan jaridar duniya.

A lokacin da za a rufe taron, Firaiministan Indiya Narendra Modi wanda shi ne shugaban na G20 zai mika jagorancin kungiyar zuwa ga Shugaban Brazil.

Shugabannin G20 wadanda ba su halarci taron ba sun hada da Shugaban Rasha Vladimir Putin da Shugaban China Xi Jinping.

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU), wadda ke da kasashe 55, ta samu gurbi a G20 bayan ta samu gayyatar Modi.

“Wannan zai kara karfafa G20 da kuma kara karfafa muryar kasashen kudancin duniya,” in ji Modi.

TRT World