Yarima maijiran gadon Masarautar Saudiyya Mohammed bin Salman ne ya yi wa Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan maraba cikin wani biki na barka da zuwa a Jidda. / Hoto: AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya isa Saudiyya a wata ziyara ta kwana uku da yake yi a yankin Gulf don kyautata dangantaka.

A zangonsa na farko na bulaguron, Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Faisal bin Farhan Al Saud da sauran manyan jami'ai ne suka yi wa Erdogan maraba a ranar Litnin a filin jirgin saman da ke birnin Jiddah.

Shugaban kasar ya isa Saudiyya ne tare da rakiyar mambobin majalisar zartarwarsa.

Daga cikin abubuwan da za a tattauna har da dangantakar yanki da ta kasa da kasa.

Bayan Saudiyya, Erdogan zai kai ziyara kasashen Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa UAE.

Karfafa dangantaka

A yayin ziyararsa kasashen yankin Gulf ukun, a baya Erdogan ya ce yana son kyautata alaka da kuma kulla yarjejeniyoyin zuba jari.

Da yake jawabi ga manema labarai a birnin Istanbul kafin fara ziyarar tasa ta yankin Gulf, Erdogan ya ce a shekarar 1929 kasarsa ta fara kulla alakar diflomasiyya da Saudiyya.

"Muna son mu fadada tushen dangantakarmu ta hanyar samun hadin kai ta wasu fannonin daban," ya kara da cewa.

Shugaban na Turkiyya ya ce, kasancewar Saudiyya kasa mai muhimmanci sosai a yankin, tana da waje na musamman a fannonin da suka shafi kasuwanci da zuba jari da sauran ayyuka na kwangila.

"Darajar ayyukan da 'yan kwangilarmu ke yi a Saudiyya a shekara 20 da suka wuce ta kai a kalla dala biliyan 25. Muna son kamfanonin Turkiyya su taka babbar rawa a fannin manyan ayyuka da Saudiyya ke yi," in ji shi.

AA