Ministan Saudiyya na ziyara a Ankara da manufar gana wa da mahukunta kan hanyoyin bunkasa dangantakar kasuwanci da diplomasiyya tsakanin kasashen biyu. Hoto: TRT World

Alakar Saudiyya da Turkiyya ta shiga wani sabon shafi na hadin kai, in ji Ministan Masana'antu na Masarautar Saudiyya.

A wata tattauna ta musamman da kamfanin dillancin labarai na Anadolu, Ministan Masana'antu da Albarkatun Kasa na Saudiyya Bandar Alkhorayef ya ce Saudiyya na da karfin gwiwa kan masu zuba jari na Turkiyya wajen assasa tubalin tattalin arziki da kasashen biyu za su habaka hadin kansu.

"Mun samu damarmaki da dama na hada kai da Turkiyya a bangaren samar da abinci da kiwon lafiya da ayyukan soji da masana'antu" in ji Alkhorayef.

Ya ce akwai kuma damar samun hadin kai tsakanin Saudiyya da Turkiyya a fannin kera jiragen sama da makamashi mai sabuntuwa da sararin samaniya.

Ministan na Saudiyya na ziyarar kwana biyar a Turkiyya, inda zai tattauna da mahukuntan kasar da 'yan kasuwa kan hanyoyin karfafa hadin kai tsakanin kasashen biyu.

"Jiragen sama da masana'antun tsaro da ci gaban karfen kera jiragen sama, wadanda kayayyaki ne da dole ana bukatar su ga masana'antu, na daga bangarorin da za mu hada kai da Turkiyya," in ji Alkhorayef.

Ya kara da cewa "Turkiyya na shigar da albarkatun man fetur sosai kasarta, za a iya aiki da Ankara wajen biyan bukatarsu a wannan bangare."

"Akwai bangarori da dama da za a iya hada kai kamar na bangaren kera motoci, Saudiyya na shirin fara kafa kamfanin motoci masu aiki da lantarki. Turkiyya na da wannan tsari, inda take samar da batiran motocin."

Hadin kan Saudiyya da Turkiyya

Kasashen Saudiyya da Turkiyya na kan hanya mai matukar muhimmanci ga kasuwancin kasa da kasa da fito tsakanin Gabas da Yamma.

"Yankin na daga tushe masu matukar muhimmanci don ciyar da masana'antunmu gaba a Saudiyya," in ji Alkhorayef. "Muna da manufar zama cibiyar safarar teku ta duniya kuma jagora a fannin masana'antu."

Ministan na Masana'antu ya kuma ce ficen yanki, kayan more rayuwa da albarkatun kasa da masarautar ke da shi ya sanya "Saudiyya ta zama babbar mai taka rawa."

Alkhorayef ya yi tsokaci kan cewa Turkiyya na da ikon kara kaimi wajen amfana da wannan yanki."

Ministan na Saudiyya ya ce alaka ta musamman tsakanin Riyadh da Ankara na bai wa 'yan kwangilar Turkiyya su samu kwangiloli a bangarori daban-daban, da suka hada da na ayyukan soji.

Ya kara da cewa "Muna aiki tare don taimaka wa wajen daga martabar kayayyakin da ake samarwa a cikin gida, yadda kamfanonin Turkiyya za su yi gogayya a Saudiyya."

Alkhorayef ya bayyana yadda kayayyakin Turkiyya suka samu karbuwa a Saudiyya.

"Akwai tattaunawa da kamfanonin Turkiyya wajen karfafa ayyuka a masarautar Saudiyya don biyan bukatar da ake da ita."

Ya ce "Dabarun habaka masana'antun Saudiyya na da manufar gabatar da sabuwar fasahar kere-kere a masana'antu, tare da assasa tushen masana'antun a Zango na Hudu na Juyin Juya Halin Masana'antu, kamar amfani da kirkirarriyar basira." "Turkiyya na da hanyoyin warware wadannan abubuwa."

Ministan masana'antun na Saudiyya ya kuma jaddada alakar kasarsa da Turkiyya "Ta haura da mai saye da sayarwa".

Ya ce "hadin kan ya hada da kafa masana'antu a cikin gida da musayar fasahar kere-kere da bayar da horo da cancanta da tabbatar da kwarewa a bangarorin bincike, da ci gaba da kirkire-kirkire,"

Alkhorayef ya kara da cewa "Saudiyya na da ikon samar da kayayyaki don bukatar kasuwanninta, a saboda haka hadin kan zai zama tushen alakarmu."

TRT World