Hare-haren Isra'ila sun kashe Falasdinawa akalla 19,667, galibi mata da ƙananan yara, tare da jikkata wasu 52,586. Hoto: OTHERS

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sake yin Allah wadai da gazawar Ƙasashen Yammacin Duniya wajen daƙile hare-haren da Isra'ila ke kai wa a Zirin Gaza na Falasdinu, yana mai cewa abin kunya ne ga bil'adama.

"Tarihi zai hukunta waɗanda suka haddasa wannan mummunan yanayi, da wadanda suka yi ƙoƙarin halasta shi, da wadanda suka yi watsi da shi," in ji Erdogan, yayin da yake magana a wajen bikin karramawar al'adu da fasaha na shugaban kasa a Ankara ranar Laraba. .

Shugaban na Turkiyya ya ƙara da cewa, "Abin kunya ne ga bil'adama kasancewar manyan ƙasashe da dama ba su da wani ƙarfi wajen tunkarar munanan hare-haren da Isra'ila ke kai wa da ya jawo kisan kiyashi da sata."

Bayan haka Erdogan ya bayyana fatansa cewa "2024 za ta kasance shekarar da azzalumai za su fuskanci hukuncin da ya dace da su, kuma za a warke raunukan waɗanda aka zalunta."

Tun bayan harin da kungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba Isra'ila take kai hare-hare babu ƙaƙƙautawa a Zirin Gaza, inda ta kashe Falasdinawa akalla 19,667, galibi mata da ƙananan yara, tare da jikkata wasu 52,586, a cewar hukumomin lafiya a yankin.

Hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza ya mayar da yankin kufai, inda rabin gidajen da ke yankin na gabar teku suka lalace, sannan kusan mutum miliyan biyu suka rasa matsugunansu a yankin da ke da yawan jama'a sakamakon ƙarancin abinci da tsaftataccen ruwan sha.

Kusan ‘yan Isra’ila 1,200 ne ake kyautata zaton an kashe a harin na Hamas, yayin da sama da mutum 130 da aka yi garkuwa da su ke hannunsu.

TRT World