"Rahoton Tarayyar Turai na 2023 game da Turkiyya, kamar rahotanni na baya, na ci gaba da nuna wariya ga Turkiyya, wanda rahoto ne da ke dauke da tsattsauran auna al'amura," in ji kakakin jam'iyyar AK a ranar Alhamis din nan.
Hukumar Tarayyar Turai a ranar Larabar nan ta fitar da rahoton da ta saba fitarwa duk shekara kan kasar Turkiyya da ke neman shiga Tarayyar, a matsayin wani bangare na Shirin Ayyukan 2023.
Ankara na sukar yadda aka dakatar da tattaunawar da ake yi da hadin kai da Turkiyya kan batutuwan da suka shafi manufofin kasashen waje da cigaban yankuna da tsaro da ayyukan soji da al'amuran sauran ɓangarori.
Abun kunya ne cewa wannan rahoto ya rawaito da yin tsokaci kan matsayin Turkyya game da kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Falasdin a matsayin abun da bai dace da ayyukan Tarayyar ba," in ji kakakin Jam'iyyar AK Omer Celik.
Ya kara da cewa "Matsayin Turkiyya zai zama abun yaba wa a wajen jama'ar Turai da na sauran duniya.
Celik ya ce Hukumar Tarayyar Turai, da kuma kasashe jagororin Tarayyar, ba su da ƙima da darajar da za su yi magana a madadin ƙimar ɗan'adam, saboda halayyar da suka nuna game da Gaza.
"Muna shaida bambanci babba tsakanin kasashen Turai da titunansu," in ji Omer Celik. "
Ya ce "Duk da kalubale daban-daban, titunan Turai sun bayyana halayyar da ta dace da dabi'un duniya masu kyau da kuma dokokin kasa da kasa game da kashe ɗan'adam da ake yi a Falasdin."
"A karo na biyu, muna sake gaishe da jama'ar Turai, yayin da muke gargadin hukumomin Tarayyar Turai game da ayyukansu, wanda za su zama baƙar lamba a tarihi."
Turkiyya ta kasance jagora wajen bayar da taimako, inda tuni ta aika da jiragen sama 10 dauke da kayayyakin da suka haura tan 230 na agaji zuwa Gaza, da aka kai ta filin tashi da saukar jiragen sama na Al Arish da ke Masar.