Ofishin jakadancin Turkiyya ya raba taimakon kayan abincin azumi a Sudan ta Kudu

Ofishin jakadancin Turkiyya ya raba taimakon kayan abincin azumi a Sudan ta Kudu

An bai wa Musulmai mabukata kunshin kayan abinci sama da 180.
Turkiyya na taimaka wa mabukata a dukkan sassan duniya/ Photo: AA

Ofishin jakadancin Turkiyya a Sudan ta Kudu y araba kunshin kayan abinci 183 ga mabukata Musulmai, a wani bangare na taimakon azumin watan Ramadhan.

Kunshin kayan abincin sun hada da man girki da wake da shinkafa da sukari da kuma garin masara.

An mika kayan abincin ga mabukatan karkashin Hukumar Hadin Kai da Cigaba ta Turkiyya (TIKA) da hadin gwiwar Cibiyar Addinin Musulunci ta Sudan ta Kudu.

Jakadan Turkiyya a Juba Erdem Mutaf ya bayyana cewa taimakon alama ce ta irin kauna da goyon bayan da Turkiyya ke nuna wa ga jama’ar Sudan ta Kudu.

Ya ce “Muna fama da radadin girgizar kasa, muna da dubban mutane da girgizar kasa ta shafa, kuma muna tallafa musu tare da ku mutanen Sudan ta Kudu”.

Mutaf ya yaba wa hukumomi da kungiyoyin farar hula na Turkiyya saboda aiki tukuru wajen isa ga marasa galihu da ke Sudan ta Kudu.

Ya kara da cewa ba kayan abinci kawai suke rabawa ba, suna kuma gudanar da aiyukan cigaba, horar da mata sana’o'i, kula da yara kanana da ayyukan rage radadin annoba a Sudan ta Kudu.

A nasa bangaren, Sakatare Janar na Majalisar Addinin Musulunci ta Sudan ta Kudu, Abdallah Baraj ya ce sun yi farin ciki matuka bisa wannan taimako da suka samu.

Ya ce, “Muna yaba wa gwamanatin Turkiyya bisa tallafa wa Musulman Sudan ta Kudu. Wadannan kayan abinci za su taimaka wa masu neman abin da za su ci.”

Ya kara da cewa wadanda suka amfana sun hada da mata, tsofaffi da mutane masu nakasa.

Daya daga cikin wadanda suka samu tallafin abincin Mohammed Maruk ya gode wa gwamnatin Turkiyya bisa wannan taimako da ta ba su a lokacin da ba su da abin da za su ci.

AA