| Hausa
TURKIYYA
3 MINTI KARATU
Netanyahu yana sukar Turkiyya ne domin ɓoye laifukan da yake aikatawa: Altun
A yayin da wasu shugabanni suke son wanzar da zaman lafiya da tsaro, wasu kuwa, irin su Netanyahu, sun fifita rashin imani da rashin mutunci da tayar-da-zaune-tsaye, a cewar daraktan sadarwa na Turkiyya.
Netanyahu yana sukar Turkiyya ne domin ɓoye laifukan da yake aikatawa: Altun
Altun ya jaddada matsayin Turkiyya na yin adawa da manufofin Netanyahu, inda ya ce ba za su daina bankaɗo yaudara da ƙarairayin da yake yi ba. / Hoto: AA / Others
10 Maris 2024

Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya caccaki Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu bisa ci gaba da yin amfani da dabarun yaudara domin janye hankalin duniya daga laifukan da ake zarginsa da aikatawa.

Altun ya bayyana haka ne a saƙon da ya wallafa a shafin X ranar Asabar, yana mai cewa babu wata yaudara ta Netanyahu da za ta sa tarihi ya manta da ɓarnar da gwamnatinsa take aikatawa a kan fararen-hular da ba su ji ba ba su gani ba a Gaza, inda ya bayyana shi a matsayin abin kunya ga ƙasarsa.

"Netanyahu ya sake sukar ƙasarmu domin ya ɓoye laifukan da yake aikatawa. Babu wata ƙarya da yaudara da za ta ɓoye kisan ƙare-dangin da ya yi wa fararen-hular da ba su da laifi. Tuni aka sani cewa shi ne shugaban da ya fi rashin imani da aka taɓa samu a wannan yanki da ma ƙasarsa," in ji Altun.

Altun ya ce akwai shugabannin da ke ƙaunar zaman lafiya da tabbatar da tsaro irin su Shugaba Recep Tayyip Erdogan waɗanda suka sanya walwalar ƴan ƙasarsu da ta maƙwabtansu a gaba kuma ya kamata a yi koyi da su.

Ya jaddada manufofin Erdogan na kare gaskiya da yin adalci a duniya baki ɗaya, yana mai fito da muhimancin adalci daga shugabanni.

Netanyahu 'shugaba ne da ya yi matuƙar gazawa'

A ɓangare ɗaya, Altun ya zargi shugabanni irin su Netanyahu da nuna son-kai da ƙeta da hana zaman lafiya a duniya domin cika burinsu na siyasa.

Duk da goyon bayan da wasu ƙasashen duniya suke yi wa manufofin Netanyahu, Altun ya yi hasashen cewa nan gaba zai yi faɗuwar-baƙar-tasa, yana mai cewa duniya ba za ta taɓa mantawa da rashin imanin da ya aikata a yankin ba.

Altun ya jaddada matsayin Turkiyya na yin adawa da manufofin Netanyahu, inda ya ce ba za su daina bankaɗo yaudara da ƙarairayin da yake yi kan yaƙin Gaza ba.

MAJIYA:TRT World