Ministocin Tsaron Turkiyya da Djibouti sun sa hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa ta soji

Ministocin Tsaron Turkiyya da Djibouti sun sa hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa ta soji

Karkashin jagorancin hafsoshin tsaron kasar biyu, an gudanar da taron tawagogin a karkashin Ma'aikatar Tsaron Turkiyya.
Ma'aikatar ta ce a karkashin jagorancin hafsoshin tsaron biyu an gudanar da wani taro na matakin tawaga. / Hoto: AA

Manyan hafsoshin tsaron Turkiyya da na ƙasar Djibouti ta gabashin Afirka sun sa hannu kan wasu jerin yarjejeniyoyi da ƙa'idoji a birnin Ankara, wadanda suka haɗa da yarjejeniyar hadin gwiwa ta horar da sojoji, da yarjejeniyar hadin gwiwar hada-hadar kudi ta soji, da kuma yarjejeniyar aiwatar da tallafin kudi.

Ma'aikatar tsaron kasar ta bayyana cewa, a hukumance Minista Yasar Guler ya yi maraba da Ministan Tsaron Djibouti Hassan Omar Mohamed a ranar Litinin, wanda ya isa birnin Ankara a matsayin baƙo, tare da bikin soji. Bayan kammala bikin, ministocin biyu sun ci gaba da taron kasashen biyu.

Ma'aikatar ta ce a karkashin jagorancin hafsoshin tsaron biyu an gudanar da wani taro na matakin tawaga.

Ma'aikatar ta ce, a taron wanda ya samu halartar kwamandan rundunar sojin ƙasa ta Turkiyya Janar Selcuk Bayraktaroglu, hafsoshin tsaron sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi uku.

Kasar Djibouti mai yawan al'umma ƙasa da miliyan guda, tana wuni muhimmin yanki a Gaɓar Tekun Aden a matsayin hanyar wucewa ta Bahar Maliya.

TRT World