Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya karɓi baƙuncin kwamitin "Kungiyar Tuntuba ta Gaza" a Taron Diflomasiyyar Antalya /Hoto: AA

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya karɓi baƙuncin kwamitin "Kungiyar Tuntuba ta Gaza" a Taron Diflomasiyyar Antalya.

Kasancewa wanda yake cikin mambobin ƙungiyar tuntuɓar juna, Ministan Harkokin Wajen Falasdinu Riyad al Maliki da Ministan Harkokin Wajen Masar Sameh Shoukry sun halarci taron a yau Juma'a, inda suka tattauna ƙoƙarin da ake na dakatar da abin da ake yi wa Falasɗinu na kisan kiyashi da ake yi a Zirin Gaza.

Ministan Harkokin Wajen Masar Sameh Shoukry ya bayyana cewa, yana matukar jin ɓacin rai saboda rashin iya ba da isasshen agajin jinƙai ga Falasdinawa a Gaza saboda mawuyacin halin da ake ciki.

"Isra'ila na burin rusa Gaza baki daya"

Ministan Harkokin Wajen Falasdinu Riyad al Maliki ya bayyana a yayin taron cewa Isra'ila ta gaza cimma ko daya daga cikin manufofinta da ta ayyana a rikicin da ake ci gaba da yi a Gaza.

Ya ce ɗaya daga cikin manufofin Isra'ila da ba a bayyana ba, shi ne yadda za a lalata Gaza gaba daya, domin wannan shi ne abin da ya sa take dagewa a yaƙin da take yi.

Ya ƙara da cewa "(Firaministan Isra'ila Benjamin) Netanyahu na son korar mutane gaba daya daga Gaza, yana so ya mayar da ita kufai.

"Idan ba za mu iya a cikin makonni biyu zuwa uku masu zuwa don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ba, to hakan na nufin za mu sake ganin wani tashin hankali, kai hari kan Rafah, wani kisan kiyashine ne, da kuma ci gaba da kisan kare dangi," in ji al Maliki a taron diflomasiyyar Antalya.

"Babban burin Isra'ila shi ne mamaye Gabar Yammacin Kogin Jordan"

Dangane da manufofin Isra'ila a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, al Maliki ya ce: "Isra'ila na da dogon lokaci ba kawai na ci gaba da zama a Yammacin Kogin Jordan ba, har ma da korar mutane daga Gabar Yammacin Kogin Jordan da kuma mamaye Falasdinawa,” ya ƙara da cewa:

"Wannan shi ne dalilin da ya sa muke ganin a kullum ana ƙwace filayen Falasdinawa a Yammacin Kogin Jordan da gina matsugunai ba bisa ƙa'ida ba da lalata gidajen Falasdinawa da hare-hare kan matsugunai, da kuma mamaye ko ina."

"Yayin da kowa ke mai da hankali kan kisan kiyashin da ke faruwa a Gaza, ya kamata mu tuna cewa ainihin manufar Isra'ila ita ce Yammacin Kogin Jordan, yankin da ake kira Yahudiya da yankin Samariya," in ji shi.

"Wadanda suke kisan gilla sun toshe kunnunwansu daga kukan da ake yi"

A yayin jawabin bude Taron Diflomasiyya na Antalya, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya bayyana cewa, "Duniyar Musulunci, Duniya ta Kudu, da kuma mutanen da suka san me suke yi na Yammacin Duniya sun tsaya tsayin daka kan Gaza, yayin da masu kisan gilla suka yi watsi da wannan kukan."

Fidan ya ƙara da cewa a ranar Juma'a, "Duk da haka, wadanda suka aikata wannan kisan gilla sun kasance sun rufe idonsu tare da toshe kunnensu.

"Za mu iya ganin cewa mutane masu daraja a Yammacin Duniya ba sa nuna halin ko-in-kula da wannan ta'asa a Gaza ba," in ji shi.

Ya ƙara da cewa, ƙona kansa da wani sojan Amurka ya yi saboda ya kasa jurewa kisan kiyashin da ake yi a Zirin Gaza alama ce da ke nuna bin dokar tsarin ƙasa da ƙasa da mutane ke so a yi.

Taron Diflomasiya na Antalya ya taɓo batutuwa daban-daban na duniya

An fara taron ne a birnin Antalya da ke Gabar Tekun Bahar Rum na Turkiyya a ranar Juma'a, wanda ya karbi bakuncin wakilai daga kasashe 147 na duniya karkashin taken taron na "Daukaka diflomasiyya a yayin rikice-rikice".

Kusan mahalarta 4,500 da suka hada da shugabannin kasashe 19 da ministoci 73, da wakilan kasashen duniya 57 ne ake sa ran za su halarci taron karo na uku, wanda aka fara a ranar Juma'a.

Taron na bana ya ƙunshi bangarori sama da 50 tare da kuma baje kolin nune-nune daban-daban.

Mahalarta taron sun hada da jami'an diflomasiyya da 'yan siyasa da ɗalibai da malamai, da wakilai daga kungiyoyin farar hula da 'yan kasuwa.

Daga cikin fitattun nune-nunen da baje kolin "Karni na Turkiyya" ya bayyana irin gudunmawar hangen nesa da Turkiyya ta bayar ga fasaha da makamashi da tsaro da masana'antu.

Taron ya kuma gabatar da "MafHar ila yau taron zai haɗa da nuna shirin "Bulletproof Dreams: Gaza Children Painters Exhibition", wato Nunin zanen Yara na Gaza, wanda Sashen Sadarwa na Fadar Shugaban Ƙasar Turkiyya ya shirya domin bayyana matsalolin jinƙai da yara ke fuskanta a Gaza.arki masu hana harsashi: nunin zanen yara na Gaza."

TRT World