Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya buƙaci mambobin G20 da su ''ƙara himma'' tare da taka rawa wajen cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, kamar yadda majiyoyin diflomasiyyar Turkiyya suka rawaito.
Fidan ya halarci wani zama na musamman a ranar Laraba, kan rawar da G20 za ta taka a tashe-tashen hankula da ke ci gaba da faruwa a duniya a taron ministocin harkokin wajen G20 a Brazil, inda ya ce "ya kamata a gaggauta dakatar da zaluncin da ake yi a Gaza."
Ya ƙarfafa wa ƙasashen duniya da G20 gwiwa kan su goyi bayan samar da ƙasashe biyu tsakanin Isra'ila da Falasdinu, in ji majiyoyin.
'Diflomasiyyar duniya tana da muhimmanci'
A ranar 24 ga Fabrairu, shekaru uku na 'aikin soji na musamman' na Rasha a Ukraine zai fara.
Hakan Fidan ya bayyana fatan Turkiyya na cewa ɓangarorin da abin ya shafa za su karkata ga harkokin diflomasiyya don samun maslaha.
Ya ƙara da cewa Ankara za ta ci gaba da gudanar da shirye-shiryenta ta wannan hanya.
Bugu da ƙari, ministan na Turkiyya ya ce ƙasashen duniya na fuskantar ƙalubale da dama da fasahohin zamani suka haifar kamar rashin daidaito da rashin adalci a duniya haɗi da taɓarɓarewar tattalin arziki da matsalolin muhalli da na fasahar leƙen- asiri.
Ya jaddada muhimmancin diflomasiyyar duniya da kuma haɗin gwiwar ƙungiyar G20 wajen bunƙasa shirye-shirye a dukkan yankunan da ke fama da rikici, a cewar majiyoyin.
Fidan ta gayyaci dukkan ɓangarorin da su yi aiki don samar da zaman lafiya da tsaro a duniya ƙarƙashin taken, "Bayyana Diflomasiyya don taƙaita rikice-rikice" a taron diflomasiyya na Antalya, wanda za a yi a ranar 1 zuwa 3 ga watan Maris.
Fidan ya gana da takwaransa na Masar
Ministan harkokin wajen na Turkiyya ya kuma gana da takwaransa na Masar Sameh Shoukry, inda suka tattauna kan matakan da za a bi wajen inganta hulɗar da ke tsakanin ƙasashen biyu a sanarwar haɗin gwiwa da suka sanya wa hannu a ziyarar da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya kai Masar a baya bayan nan, kamar yadda majiyar diflomasiyyar Turkiyya ta bayyana.
Ministocin sun kuma yi musayar ra'ayi kan halin da ake ciki a Gaza, da kuma matakan da za a ɗauka na kai ƙarin agajin a yankin Falasɗinu da aka yi wa ƙawanya.
Majiyoyin sun bayyana wasu batutuwan da ke cikin ajandar taron waɗanda suka shafi yankin, ciki har da halin da ake ciki a Libya.
Shoukry zai kuma halarci taron diflomasiya da za a yi a Antalya a ranar 1 zuwa 3 ga Maris. Kazalika ana sa ran zai halarci taron ƙolin Gaza, wanda zai samu halartar mambobin ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Musulmai ta OIC da kuma ƙungiyar ƙasashen Larabawa.
Ganawa da takwaransa na Amurka Blinken
Tun lokacin da Isra'ila ta fara kai hare-hare kan Falasɗinu, Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya yi ta ganawa da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken inda suka yi musayar ra'ayi kan matakan da za a ɗauka don tabbatar da an tsagaita wuta a Gaza.
Ministocin harkokin wajen biyu sun kuma gana a Brazil inda rahotanni suka ce Fidan ya buƙaci Blinken ya matsa lamba kan Isra'ila ta daina zubar da jini musamman a Gaza.
Majiyoyin diflomasiyyar sun ce Fidan da Blinken sun kuma tattauna kan yaƙin da ake yi a Ukraine, da shirin faɗaɗa NATO, da kuma batun tattaunawar zaman lafiya tsakanin Azabaijan da Armeniya, da sauran batutuwan yankin.
A cewar majiyoyin, manyan jami'an biyu sun kuma taɓo batun jadawalin babban taron da za a gudanar nan gaba.
Ganawa da takwarorinsa na Jamus da Bolivia
Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya yi wata ganawar sirri da takwarorinsa na Jamus da Bolivia.
Fidan da ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock sun tattauna kan dangantakar da ke tsakanin Turkiyya da Jamus kamar yadda majiyar diflomasiyyar Turkiyya ta bayyana.
Fidan ya sanar da Baerbock matsayar Turkiye game da wasu takamaiman matakai da za a iya ɗauka don kawo ƙarshen "tashin hankali" a Gaza.
A wata ganawa ta daban, Fidan da takwaransa na Bolivia Celinda Sosa Lunda, sun amince da ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ƙasashensu, musamman a fannonin masana'antun da tsaro da kiwon lafiya da kuma al'adu.
Har ila yau, sun tattauna matakan da za a ɗauka na bunƙasa harkokin cinikayya tsakanin ƙasashen biyu.
Fidan da Lunda sun kuma tattauna batutuwan da suka shafi yankunansu da duniya baki ɗaya, ciki har da tashe-tashen hankulan da ke ci gaba da faruwa a Gaza, a cewar majiyoyin.
Haka kuma za a duba batun kafa cibiyar raya al'adun Turkiyya ta Yunus Emre a babban birnin ƙasar Bolivia La Paz.