Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan da takwaransa na Iran Hossein Amirabdollahian sun tattauna ta wayar tarho akan batutuwan da suka faru a yankin a baya-bayan nan, kamar yadda majiyoyin diflomasiyyar Turkiyya ta bayyana.
Majiyoyin a ranar Juma'a sun ce an yi tattaunawar wayar ne bisa bukatar bangaren Iran, ba tare da karin bayani ba.
Tun da farko Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta ce tana sa ido sosai kan al'amuran da suka faru a yankin, tare da yin kira ga dukkan bangarorin da su guji daukar matakan da za su haifar da rikici mai tsanani.
Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce, "Bisa lamurra na baya-bayan nan, yana kara fitowa fili cewa tashe-tashen hankulan da tun farko suka haddasa ba bisa ka'ida ba sakamakon harin da haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai kan ofishin jakadancin Iran da ke Damascus na iya rikidewa zuwa wani rikici na dindindin."
Ya kamata kasashen duniya su mayar da hankali wajen dakatar da kisan kiyashin da ake yi a Gaza da kuma tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankinmu ta hanyar kafa kasar Falasdinu.
Rikicin Isra'ila da Iran
A ranar Asabar ne dai rikici ya ɓarke tsakanin Iran da Isra'ila bayan da Tehran ta ƙaddamar da wani jirgin yaƙi mara matuƙi da makami mai linzami a matsayin martani ga harin da aka kai karamin ofishin jakadancinta da ke Siriya a ranar 1 ga Afrilu, wanda ya yi sanadiyar mutuwar jami'an sojan Iran bakwai da suka hada da manyan kwamandoji biyu.
Kafofin yada labaran Amurka na cewa, Isra'ila ta kai wani "taƙaitaccen hari" a cikin Iran da sanyin safiyar Juma'a. Har yanzu dai babu wani bayani a hukumance daga Isra'ila.