Ministan Harkokin Wajen Turkiyya da Sakatare Janar na  MDD Guterres sun tattauna kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya da Sakatare Janar na  MDD Guterres sun tattauna kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Fidan da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya sun tattauna kan kan halin da ake ciki a yankin Gaza, a cewar majliyoyin diplomisiyyar Turkiyya.
A wata tattaunawa ta waya ranar Litinin, Fidan da Guterres sun yi kuma tattauna kan halin da ake ciki a Gaza. / Hoto: AA Archive

Ministan Harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya tattauna kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antoniyo Guterres, a cewar majiyoyin diflomasiyyar Turkiya.

A wata tattaunawa ta waya ranar Litinin, Fidan da Guterres sun yi kuma tattauna kan halin da ake ciki a Gaza.

Batun Cyprus da safarar teku cikin aminci a Bahrul Aswad na daga cikin batutuwan da aka tattauna, a cewar majiyar.

Tehran ta kai hare-hare sama da 300 da makamai masu linzami da jirage marasa matuka a fadin kasar Isra'ila a yammacin ranar Asabar a matsayin ramuwar gayya kan harin da jiragen Tel Aviv suka kai kan karamin ofishin jakadancin Iran da ke Damascus babban birnin kasar Syria, a ranar 1 ga Afrilu inda dakarun kare juyin juya halin Musulunci bakwai, ciki har da janar-janar guda biyu suka mutu.

Dangane da abubuwan da suka faru a yankin gabas ta tsakiya,Turkiyya ta ce za ta ci gaba da kokarin hana afkuwar wani tsari da zai lalata zaman lafiyar yankin har abada da kuma haifar da rigingimu a duniya.

Ankara ta ce "tana sake aikewa da sakwanni karara ga mahukuntan Iran da kuma kasashen yammacin duniya da ke da tasiri a kan Isra'ila, don yin kira ga kowa da kowa da ya kawo karshen tashin hankalin".

TRT World