Kamfanin Meta ya cire rahoton TRT kan yadda Isra'ila ke musguna wa 'yan jarida. / Hoto: AA

Kamfanin Meta mamallakin Facebook ya cire wani rahoto na musamman da sashen Larabci na TRT ya saka wanda ke nuna irin cin zalin da Isra’ila ke aikatawa kan ‘yan jarida a Gaza da kudancin Lebanon, inda Meta ɗin ke iƙirarin rahoton na ƙara ɗaukaka muggan mutane da ƙungiyoyi.

A ranar 30 ga watan Agusta, sashen Larabci na TRT ya fitar da rahoton na bidiyo na musamman mai taken “Kisan kiyashi kan aikin jarida,” wanda ya yi ƙarin haske dangane da irin gwagwarmayar da ‘yan jarida da ke bayar da rahoto game da Gaza da kudancin Lebanon ke yi.

Rahoton na musamman ya fito da irin kisa da sojojin da ke mamaya ke yi kan ‘yan jarida tun daga 7 ga Oktoba, inda ya fito da labarai game da ‘yan jaridar da aka kai wa hari a lokacin da suke gudanar da ayyukansu.

Rahoton wanda aka shafe kusan wata uku ana aiki a kansa, an yi shi ne a cikin yanayi na hatsari, kamar yadda daraktan da ya shirya rahoton Khaldoum Fahmawi ya shaida wa Al Jazeera da Reuters da AFP a kudancin Lebanon.

Rahoton ya kuma yi bayani kan yadda sojojin Isra'ila ke kai wa 'yan jarida hari a gidajensu da kuma kisan gillar da ake yi wa iyalansu.

Rahoton ya yi ƙarin haske dangane da iyalan ɗan jaridar nan da ya yi shahada mai suna Mustafa Sawaf da kuma kisan gillar da aka yi wa iyalansa su 47, daga ciki har da ‘ya’yansa biyu, Marwa da Monstaser ta hanyar amfani da jirgi maras matuƙi.

A cewar Ismail Al-Thawabteh, Darakta Janar na ofishin yada labarai na gwamnati, Isra’ila ta kashe ‘yan jarida 172 saboda harin da ta kai a Gaza.

Ya kara da cewa, "Takardun sun nuna Isra’ila ta kama 'yan jarida 36 a lokacin kisan kare dangi a Gaza." Daga cikin wadannan, an saki 'yan jarida hudu, yayin da 32 ke ci gaba da zama a gidan yari.

TRT World