Tashar ya da labarai mallakar gwamnatin Turkiye TRT, za ta taimaka wajen sake farfado da al’adar Somaliya tareda horar da masu shirya fina-finai don samar da wasannin kwakwayo masu inganci sosai, wanda hakan mashahuri kafin yakin basasar da ya barke a 1990.
Kakakin fadar shugaban kasar Somaliya Abdirashid Mohamed Hashi ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa “Mun hadu da daraktocin tashar TRT, kuma za su taimaka mana wajen farfado da al’adarmu, masana’antar kade-kade da shirya fina-finai.”
Hashi ya kara da cewa “Za a fassara wasannin kwaikwayo na Turkiye zuwa yaren Somaliya don tabbatar da musayar al’adu a tsakanin kasashen biyu.”
Ya ce “Idan ka je Turkiye kuma ka samu damar ziyartar Istanbul ko Ankara, za ka yadda jama’ar Somaliya suka shaiga cikin al’umar, suna yin kasuwanci, suna zuwa jami’o’i don ilimi, kuma sama da haka ma muna da jirgin saman Turkiye da yake zuwa Mogadishu kowacce rana dauke da fasinjojin Somaliya.”
Somaliya da Turkiye sun karfafa alakarsu a 2011 bayan da Shugaban Kasar Turkiye Recep Tayyip Erdogan ya ziyarci kasar a matsayin shugaba da ba dan Afirka ba da ya kai ziyara kasar a cikin sama da shekaru 20.
Masan’antar fina-finai
Hashi ya kuma ce “Masana’antar shirya fina-finai ta Turkiye ta zama abun sauya fasali a kasar, inda sauran fina-finan kasashen waje suke rasa makama. A baya ‘yan Somaliya na kaunar kallon fina-finan Bollywood, amma a yanzu fina-finan Turkiye ne suka maye gurbinsu.”
A wannan shekarar, bukatar neman koyon harshen Turkanci a tsakanin matasa, musamman ma mata manya da kanana, ta ninka sosa, saboda kallon fina-finan Turkiye.
Zaynab Abdi Adnan na kaunar fina-finan Turkiye. Ta bayyana cewa tana kallon fina-finan tun kusan shekaru uku, kuma ta koyi yadda ake sadarwa da yaren Turkanci.
Ta ce “Ina son yadda suke mu’amala cikin fim musamman kan abun da ya shafi soyayya. Kawai ina so, a yanzu haka na kamu da maitar kallon wani shiri na tarihi mai taken Alparslan: Buyuk Selcuklu, kuma jarumin da ya fi kowanne a wajena shi ne (wanda ya fito a matsayin) Alpagut.”
‘Istanbul’
Wani dattijo a Mogadishu Ahmed Osman ya shaida cewa “ Idan kana son ka san irin tasirin da Turkiye ta yi a Somaliya, to ka bincika sunayen mata a kasar.”
Ya ce daya daga cikin sunayen mata mafi shahara a kasar shi ne’Istanbul’.
Dattijon ya kara da cewa “Muna da alaka ta fuskar addini, kuma ina farin ciki da ganin kasar Musulmai tana da wannan tasirin a kanmu, saboda kafin zamaninmu, Kasashen Yamma ne ke da tasiri kamar al’adun Italiya da sauran su.”
Bukin murna na musamman
A wannan shekarar, Somaliya ta yi bukin cika shekaru 11 da kulla alakarta ta musamman da Turkiye.
Jami’an diplomasiyya na kasashen waje, manyan jami’an gwamnatin Somaliya da Jakadan Turkiye a Somaliya na daga cikin manyan baki da suka halarci bukin a Mogadishu, inda maraya da mawakan gargajiya daga Turkiye suka cashe a filin Halane wanda ke dauke da helkwatar Majalisar Dinkin Duniya a babban birnin Mogadishu.
Hashi ya ce “An gaiyaci mawakan Somaliya da makadan Turkiye don su nuna yadda musayar al’adu tsakanin Somaliya da Turkiye yake aiki, kuma dukkan baki da sauran mahalarta sun gamsu tare da yin mamaki da cashewar da aka yi.”