Matar Shugaban Kasar Turkiyya Emine Erdogan ta mika sakon murnar zagayowar Ranar Mata ta Duniya, wato bikin da ake yi duk shekara dangane da nasarorin da mata suke samu.
“A wannan rana ta Mata ta Duniya ina farin cikin taya mata masu tsayuwar daka da ke kawo sauyi da ci gaba murna,” kamar yadda Emine Erdogan ta bayyana a shafinta na X a ranar Juma’a.
Ta ce mata suna shuka iri a cikin kasa kuma suna da kyakkyawan fata ga al’umma, suna nuna tasirinsu a kowane fanni, “su ne ginshikin zaman lafiya mai dorewa da adalci a duniya.”
“Duk wata nasara tana samuwa ne saboda jajircewarsu, muna da kwarin gwiwar hango makomarmu,” in ji Emine Erdogan.
Kowace ranar 8 ga watan Maris, ana murnar zagayowar bikin martaba nasarorin da mata suka samu da kuma wayar da kan jama’a kan daina nuna musu wariya.