Turkiyya ta buƙaci ƙawayen ƙungiyar tsaro ta NATO da su ɗauki mataki a kan cin zalin da Isra'ila ke yi a Gaza, kamar yadda Shugaban Majalisar Dokokin ƙasar Numan Kurtulmus ya faɗa.
"Mu, mambobin ƙungiyar tsaro mafi girma a duniya, ba za mu iya yin biris da ɗaya daga cikin manyan batutuwan da suka fi ɗaukar hankali a duniya ba, da gaggarumin bala’in ɗan'adam da ke afkuwa a Gaza.
"Dole ne a daina wannan zubar da jini da kisan kiyashin da Isra'ila ke yi," a cewar Kurtulmus a taron 'yan majalisar dokokin NATO a Amurka ranar Talata.
Kurtulmus yana ziyara ne a Amurka har zuwa ranar 10 ga watan Yuli domin halartar taron, wanda ya hada shugabannin majalisar wakilai daga kasashe 32 na NATO da Ukraine, ciki har da shugabannin majalisar dokoki 23.
Hatsarin rikiɗewar rikicin zuwa yaƙin yanki
"Akwai matukar hadari ga wannan lamarin ya rikide zuwa yaƙin yanki. A tattaunawar da za mu yi kan tsaro a duniya, dole ne mu daidaita kanmu da gaba daya na bil'adama da ke tsayawa wajen tabbatar da gaskiya da adalci."
"Muna kira ga ƙawayenmu da su ayyana cewa 'ba za a ƙyale gwamnatin Netanyahu ta ci gaba da cin zali ba," ya ƙara da cewa.
Kurtulmus ya jaddada cewa Turkiyya ta buƙaci a tsagaita wuta da gaggawa, a ba da damar kai kayan agaji sannan a samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu a matsayin mafita ta dindindin ga yaƙin Falasɗinu da Isra'ila.