Turkiyya ta kara yawan wutar lantarkinta da megawatts 2,858 ta hanyar amfani da makamashi mai maras gurɓata muhalli, wanda hakan ya sa ta samu haɓaka da kaso 99.5 cikin 100 ta ɓangaren makamashin, kamar yadda Alparslan Bayraktar ya bayyana, ministan makamashi da albarkatun kasa na Turkiya.
Makamashi maras gurɓata muhallin da aka saka a kasar ya kara megawatts 2,845 a shekarar da ta gabata, inda adadin wutar lantarkin da ake amfani da shi ya kai terawatts 2,845, kamar yadda Bayraktar ya shaida a wata sanarwa a ranar Litinin.
Sakamakon sabbin kayayyakin lantarkin da aka saka, adadin kayan lantarkin da aka saka sun kai na megawatts 106,668 inda na makamashi maras gurɓata muhalli yake da megawatts 59,236.
Ya ce kaso na makamashin da ake sabuntawa a fannin samar da wutar lantarki ya kai kashi 42 cikin 100, kuma abin da ake so shi ne a kara yawan wannan kaso zuwa kashi 55 cikin 100 nan da shekarar 2035.
Har ila yau, kasar na da burin kara yawan kason da ake sabuntawa na makamashin lantarki zuwa kashi 65 a shekarar 2035 daga kashi 56 a shekarar 2023.
A bara, wutar lantarkin da ake samu ta hanyar karfin iska da hasken rana ya kai megawatt 11,803 da kuma 11,315, bi da bi.
Na’urar Biogas da aka saka ya samar da megawatts 2,076 a shekarar da ta gabata, yayin da karfin wutar lantarki ya kai megawatt 1,691. Ƙarfin wutar lantarki, tare da kaso mafi girma a tsakanin kafofin da ake sabuntawa, ya kai megawatts 31,963.