Majalisar Dokokin Turkiyya ta amince da kudirin dokar shiga kasar Sweden cikin kungiyar tsaro ta NATO.
Bayan kada kuri'a a Majalisar Dokokin Turkiyya a ranar Talata, Hungary ta zama mamba daya tilo a kungiyar NATO da har yanzu ba ta amince da yunkurin Sweden na shiga kungiyar ba.
A watan Oktoban 2023, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shiga kungiyar tsaro ta NATO ta Sweden tare da mika ta ga majalisar dokoki.
Finland da Sweden - ƙasashen Nordic da ke kusa da ko kuma masu iyaka da Rasha - sun nemi zama mamba a NATO jim kaɗan bayan Rasha ta ƙaddamar da yaƙin Ukraine a cikin Fabrairun 2022.
A watan Maris na 2023 ne Turkiyya ta amince da zammowar Finland mamba a cikin ƙawancen, amma ta ce tana jiran Sweden ta mutunta yarjejeniyar da aka cimma a watan Yunin 2022 don magance matsalolin tsaro na Ankara.
Dole ne sai duka mambobin ƙungiyar na yanzu sun amince da duk wata sabuwar mamba, kafin a shigar da ita NATO, ciki har da amincewar Turkiyya, wadda mamba ce a ƙungiyar kawance tsawon sama da shekaru 70, wadda ita ke da karfin soja na biyu mafi girma.