Masu goyon bayan kungiyar PKK sun kai hari kan ‘yan Turkiyya masu zabe a birnin Marseille na Faransa.
Majiyoyi na diflomasiyya sun shaida wa sashen TRT na Faransa cewa akwai adadin da ba a kididdige ba na ‘yan Turkiyya da aka kai wa hari a kusa da wata rumfar zabe a birnin a ranar Litinin da Yamma.
Sai dai babu wanda ya ji rauni a cikin masu zaben, kamar yadda majiyoyin suka kara da cewa.
Jami’an tsaro da ofishin jakadanci babba da karami a kasar sun dauki matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron rumfunan zabe da ‘yan kasar.
Jakadan Turkiyya a Faransa, Ali Onaner, shi ma ya kai ziyara wurin da lamarin ya faru.
A watan Maris din bana, Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta caccaki Majalisar Dattawan Faransa kan gayyatar wasu da ke da alaka da kungiyoyin ta’adanci na PKK/YPG da kuma ba su ‘lambar yabo”.
A hare-haren da ta shafe sama da shekara 35 tana kai wa a kan Turkiyya, PKK wadda Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai duka suka ayyana a matsayin kungiyar ta’addanci ta yi sanadin mutuwar sama da mutum 40,000 ciki har da mata da yara.
Tsakanin 27 ga watan Afrilu zuwa 9 ga watan Mayu, sama da mutum miliyan 3.4 ‘yan Turkiyya da ke zama a kasashen waje 73 aka kira domin jefa kuri’a a zaben 2023 na shugaban kasa da na ‘yan Majalisar Dokokin kasar tasu.
Masu zabe za su zabi daya daga cikin mutum hudu: Shugaba mai ci Recep Tayyip Erdogan da Muharrem Ince da Kemal Kilicdaroglu da kumaSinan Ogan. Kusan mutum miliyan 1.5 ne suka jefa kuri’arsu a zaben da ya gabata.
A Faransa, inda ‘yan Turkiyya 800,000 ke zaune a can, akwai masu zabe kusan 397,086.
Hukumomi sun bayyana cewa Turkiyya ta samar da rumfunan zabe a wurare 156 a kasashe 73.