A watan Disamban 2019 ne Kungiyar Hadin Gwiwar Samar da Motoci a Turkiyya (TOGG) suka kaddamar da mota mai aiki da lantarki ta farko kirar kasar.

Kamfanin kera motoci masu aiki da lantarki na farko a Turkiyya Togg ya fitar da sabuwar mota samfurin Sedan T10F a wajen baje-kolin CES 2024, babban taron baje-kolin kayan lataroni da fasahar kere-kere da ake yi a Las Vegas da ke Amurka.

A tattaunawar musamman da TRT World ta yi a ranar Talata da Shugaban kamfanin Togg Mehmet Gurcan Karakas ya bayyana cewa motarsu mai aiki da lantarki ta biyu samfurin T10F ta zama wata babbar nasara ga kamfanin.

Karakas ya kara da cewa "na yi amanna cewa wannan abu namu ne baki daya, rana ce ta farin ciki," inda ya kuma fadi yadda mutane da dama suka nuna shakku kan kera wannan samfurin a lokacin da suka fara aiki shekaru biyar da rabi da suka wuce.

A wata makala mai taken "Motar wata duniyar," marubuci a jaridu dan kasar Italiya Messaggero ya bayyana cewa Turkiyya ba ta fita daga fagen samar da motoci ba, kuma ta kasance cibiya mai muhimmanci wajen samar da kayayyaki, saboda kasancewar ta mahadar nahiyoyi biyu.

Makalar ta kuma bayyana cewa matukar Turkiyya na alfahari da fara tuka mota kirar kasar ta Togg, kuma za a kara yawan motocin da 200,000 nan da wani dan lokaci, tare da fara fitar da ita zuwa kasashen waje nan da 2030 sama da motocin Togg miliyan daya ne za su dinga yawo a kasashen Turai."

Komai a Turkiyya aka samar da shi

Stellantis, Ford, Hyundai, Renault, Toyota, da Volkswagen na daga masu taka rawa a wannan fanni a Anatoliya su kadai ko tare da hadin gwiwar masu zuba jari a cikin gida, in ji makalar.

Sakamakon haka, a shekarar 2023 an samar da motoci sama da miliyan daya da rabi a Turkiyya, kuma wannan adadi ya ninka wadanda aka samar a Italiya da ma Ingila.

Makalar ta kara da cewa Turkiyya na na cikin kasashen duniya 10 da suka fi samar da kayayyaki.

Makalar ta ci gaba da cewa wannan ma bai ishi shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ba, wanda ya mayar da hankali ga samar da kamfanin da komai nasa daga Turkiyya ya fito.

A rubutun an kuma bayyana cewa "A 2018, ya ja ra'ayin mafi yawan kungiyoyin masu masana'antu da juya kudade kan su hada karfi da karfe don samar da motoci a kasar."

A kasa da shekara hudu, Kungiyar Samar da Motoci na Hadin Gwiwa ta Turkiyya (TOGG) ta fitar da samfurin mota na farko na T10X.

Togg sun gabatar da samfurin motar farko mai aiki da lantarki a watan Disamban 2019.

TRT World