Altun ya bayyana fata mai kyau game da sauyin halayya a tsakanin masata a Amurka game da rikicin Isra'ila-Falasdin. / Hoto: AA

Fahrettin Altun, Shugaban Sadarwa na Turkiyya, ya bayyana jawabin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a Majalisar Dokokin Amurka a matsayin babbar ƙazanta ga zauren dokokin, wanda ke ikirarin kare hakkokin ɗan'adam da darajojin dimokuradiyya.

"Jawabin Firaministan Isra'ila ga Majalisar Dokokin Amurka babbar ƙazanta ce ga zauren na dokoki da ke ikirarin kare hakkokin ɗan'adam da aiki da ka'idojin dimokuradiyya.

Sakamakon karbar bakuncin dan siyasar da ke da alhakin aikata laifukan yaki, Washington na aike wa duniya sakon cewar ba ta wani damu da rayukan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba," in ji Altun a wani sako da ya fitar ta safinsa na X a ranar Alhamis.

Altun ya soki Majalisar Dokokin Amurka saboda bai wa Netanyahu damar yada farfaganda, a yayin da ake wulakanta masu zanga-zanga a Amurka.

"Wasu 'yan siyasar Amurka da ke hada baki da gwamnatin Isra'ila sun aikata laifukan yaƙi don bukatu na siyasa za su janyo zubar da mutuncin Amurka a duniya."

'Majalisar na ƙara tunzurawa da ƙarfafa wannan yaƙi'

Duk da goyon bayan da Netanyahu ya samu, Altun ya yaba wa 'yan tsirarun 'yan siyasar Amurka da suka yi zanga-zanga ko kalubalantar kalaman na Firaministan Isra'ila.

Ya yabi wadannan ɗaiɗaikun mutane saboda matsayar da suka dauka, yana mai cewa jawabin na dauke da 'tsagwaron ƙarairayi" da "tsana ga Falasdinawa", ya kuma soki yadda Netanyahu ya dabbantar da Falasdinawa da ke karkashin mamaya."

"Sojojin Isra'ila karkashin gwamnatin Netanyahu na aikata munanan laifukan yaki da ba a fada a Falasdinu. Majalisar Dokokin Amurka ta bayar da dama da karfafa gwiwar yin wannan yaki ta hanyar bayar da taimakon kudade, makamai da harsasai ga Isra'ila.

"Yunkurin hana bayar da wannan taimako ya ci tura. Dole a dakatar da wannan idan har Amurka na da manufar ikirarin duk wani nau'i na tarbiyya ko samun halasci a fagen kasa da kasa," in ji Altun.

Kokarin Turkiyya na warware rikicin ta hanyar kafa kasashe biyu

Altun ya bayyana fata mai kyau game da sauyin halayya a tsakanin masata a Amurka game da rikicin Isra'ila da Falasdinu, yana mai jaddada yadda suka fahimci gaskiya game da mamaya da ƙarar da al'umma da kisan kiyashi a Falasdinu.

Ya jaddada cewa halin da ake ciki a yanzu ba mai ɗorewa ba ne, ya kuma yi hasashen Falasdinawa za su samu cikakken 'yanci.

Ya bukaci 'yan siyasar Amurka su fahimci cewar goyon bayan gwamnatin Netanyahu ya saɓa wa bukatar Amurka ta samun daraja a duniya.

A wani abu mai kama da nuna goyon baya, Altun ya sake tabbatar da kokarin Turkiyya na kawo maslahar warware rikicin na Isra'ila da Falasdinu.

Ya ce "Mun sake nuna goyon baya ga wadanda suke nuna bukatar a yi maslaha a warware rikicin Isra'ila da Falasdinu.

"Za mu yi aiki tukuru don tabbatar da hakan ko da gwamnatin Netanyahu da ƙawarta Majalisar Dokokin Amurka na adawa da hakan."

Altun ya ƙarƙare sukar amfani da zarge-zarge ƙyamatar Yahudawa don rufe bakin masu sukar Isra'ila, inda ya kuma yabi yadda kasashen duniya ke ƙara fahimtar tasiri da illolin hare-haren Isra'ila kan fararen hula da ba su aikata laifin komai ba.

Ya zayyana kokarin Turkiyya na warware rikicin ta hanyar kafa kasa biyu, inda za a samu Falasdinu mai ikon mulki da zama cikin lafiya tare da maƙwabtanta.

Ya ƙara da cewa "Tunanin duniya na ga bangaren kubutar da Falasdinawa. Babu dalilin ƙarar da al'umma da kisan kiyashi."

TRT World