Bayraktar ya kuma sanar da ƙaddamar da sabon hadin kai na haƙar ma'adanai da Somaliya bayan taron. / Hoto: AA

Ministan Makamashi da Ma'adanai na Turkiyya Alparslan Bayraktar ya sanar da cewa jirgin ruwan Oruc Reis ya kammala kashi 50 cikin 100 na binciken ƙarƙashin ƙasa da yake yi a tekunan Somaliya.

Jirgin ruwan na Turkiyya mai binciken ƙarƙashin teku, Oruc Reis ya isa tashar jiragen ruwa ta Mogadishu a watan Oktoban bara don gudanar da ayyukansa na gano fetur da gas a gaɓar tekun Somaliya.

Bayraktar ya gana da sabon Ministan Fetur da Ma'adanai na Somaliya Dahir Shire Mohamed da tawagarsa a Istanbul, kamar yadda ministan Turkiyyan ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma'a.

Ministocin biyu "sun tattauna kan mataki na gaba na ayyukan binciken da kuma sabbin haɗin gwiwar da za mu iya samarwa a ƙasar."

Bayraktar ya kuma sanar da ƙaddamar da sabon hadin kai na haƙar ma'adanai da Somaliya bayan taron.

"Za mu cigaba da ƙoƙarinmu na samar da haɗin kai a fannin makamashi da haƙar ma'adanai har zuwa matakin da ya kamata na inganta kyakkyawar dangantakar ƙasashenmu," ya ƙara da cewa.

Oruc Reis yana gudanar da bincike nau'i uku a ruwan Somaliya, inda yake tattara bayanai kan fetur da gas a tsawon lokaci na aƙalla tsawon wata shida zuwa bakwai.

Za a fayyace waɗannan bayanai a babban birnin Turkiyya Ankara don gano wuraren da za a iya tonowa.

TRT World