Jirgi mara matuƙi, Bayraktar AKINCI, na kamfanin Baykar Technologies na ƙasar Turkiyya ya yi nasarar gwajin harba wani makami mai linzami samfurin IHA-122 kwanakin baya.
Baykar, kamfanin da ke ƙera jirage marasa matuƙa na kasar Turkiyya, ya wallafa wani sako a shafinsa na X inda ya bayyana irin nasarorin da ya samu, kana ya fitar da bidiyon yadda ya yi gwajin.
Makami mai linzami samfurin IHA-122, wanda kamfanin tsaro na Roketsan ya ƙera, yana sauka a wurin da aka harba shi ba tare da kuskure ba, sannan yana da saurin gaske ya yin harbi, kuma yana da iya yin wasu dabaru na musamman na cim ma burinsa.
Selcuk Bayraktar, shugabannin fannin fasaha na Baykar, ya wallafa biyoyin gwajin harba makamin mai linzamin samunfurin IHA-122 daga AKINCI UCAV a shafinsa na X, gwajin da aka yi wa laƙabi "Golden Age of Turkish Aviation."
A saƙon da ya wallafa a shafin X, Murat Ikinci, janar manaja na kamfanin Roketsan wanda ke ƙera makamai masu linzami na Turkiyya, ya bayyana cewa, "Muna alfaharin samun ci-gaba a kan turbar da ƙasarmu ta tsara kan harkokin fasaha."
Ikinci ya ƙara da cewa, "Makaminumu mai linzami samfurin IHA-122 wanda AKINCI UCAV ya yi gwajin harbawa ya yi nasarar kammala zagaye. Ina taya murna ga kowa da kowa."
Jirgi mara matuƙi na AKINCI jirgi ne mai tashi sama sosai kuma yana da juriya inda yake da nauyin kilogiram 6,000 kilograms, idan aka kwatanta shi da nauyin jirgin TB2 mai nauyin kilogiram 700. AKINCI yana iya ɗaukar abubuwa masu nauyin kilogiram 1,500, wato ninki 10 kenan idan aka kwatanta da TB2.