Mataimakin shugaban Jam’iyyar AK Party kuma mai magana da yawun jam’iyyar Omer Celik ya caccaki wadanda suka yi shiru kan zaluncin da Isra’ila ke yi a Gaza, inda ya kira gwamnatin Benjamin Netanyahu da “injin kisa”.
“Bayan duk wani kisan kiyashi, Kasashen Yamma ne ke goyon bayan wannan injin din na kisa domin aikata karin kashe-kashe da sunan ‘Isra’ila na da ‘yancin kare kanta’,” in ji Celik a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Asabar.
Ya bayyana cewa wadanda suke kare Isra’ila kan cewa tana kare kanta ne da sunan daukar rayuwar mutanen Gaza na daga cikin wadanda suke aikata laifukan cin zarafin bil adama.
Duk da cewa Netanyahu na tafiya kan “tsarin kisan kiyashi”, amma har yanzu kasashen Yamma ba su ce komai kan hakkin bil adama da doka ba, in ji Celik.
Da yake jaddada “dabbacin” Isra’ila da masu goyon bayanta na Yammacin Duniya kan kaddamar da yaki kan daukacin bil’adama, Celik ya ce: "Wannan yaki ba kawai a kan Gaza ba ne har ma a kan dukkan dan’adam.
"Duk wanda ya goyi bayan Isra’la na kare kanta ba tare da magana a kan damar da ‘yan Gaza ke da ita ba ta gudanar da rayuwa" yana goyon bayan kisan kare-dangi.
"Duk wanda ya ce 'Ba mu tsawatar wa Isra’ila ba' bayan kisan da take yi wa kananan yaran da ba su da hannu a wanna rikici, to yana yaki ne da dan’adam." Celik ya ce Turkiyya ta zama “murya ga dan’adam” ba kamar Yammacin Duniya da ke goyon bayan dabbacin ba.
Shirin da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sanar yana da “muhimmanci ga gwagwarmayar kare bil adama daga dabbanci da kuma kare marasa laifi,” kamar yadda ya kara da cewa.
Sojojin Isra’ila sun kara fadada hare-haren da suke kaiwa ta sama da kasa kan Gaza, wadda ake kai wa hare-hare ba kakkautawa tun bayan harin ba-zata da Hamas ta kaddamar a ranar 7 ga watan Oktoba.
Kusan mutum 10,800 aka kashe zuwa yanzu sakamakon wannan rikici, daga ciki har da Falasdinawa 9,227 da kuma ‘yan Isra’ila kusan 1,540.
A halin yanzu ana fama da karancin kayayyakin amfanin yau da kullum a Zirin Gaza mai mutum miliyan 2.3 sakamakon irin kawanyar da Isra’ilar ta yi wa Gaza, wanda hakan ke kara adadin wadanda suke mutuwa da kuma rasa muhallansu.