Isra'ila na son boye munanan laifukanta ta hanyar sukan Shugaba Erdogan: Jami'an Turkiyya

Isra'ila na son boye munanan laifukanta ta hanyar sukan Shugaba Erdogan: Jami'an Turkiyya

Isra'ila na da hannu cikin laifukan da suka bar "baƙin maki a tarihin ɗan'adam," in ji kakakin jam'iyyar AK Party Omer Celik.
Omer Celik ya yi tir da kisan kiyashin da Isra'ila ke kai wa kan dubban faraen hula da suka hada da mata da yara. Hoto: AA Archive

Jami'an Tel Aviv sun yi ƙoƙarin ɓoye laifukan da Isra'ila ke ci gaba da yi a yaƙinta da Gaza ta hanyar kai wa shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan hari, in ji kakakin jam'iyyar AK ta Turkiyya.

"Rudun da Firaiministan (Benjamin) Netanyahu na gwamnatin Isra'ila mai shan jini da kuma Ministan Harkokin Wajensa Eli Cohen suka shiga na ƙoƙarin sukar Recep Tayyip Erdogan, wani yunƙuri ne na ɓoye laifukan da suka aikata wanda wata rana za a hukunta su a kansu," Omer Celik ya rubuta a shafin X ranar Alhamis.

Ya ce Isra’ila na da hannu cikin laifukan da suka bar “bakin maki a tarihin ɗan'adam” ta hanyar rusa masallatai da coci-coci da asibitoci yana mai cewa gwamnatin Isra’ila ta kashe dubban fararen hula da suka haɗa da mata da ƙananan yara.

"Shugabanmu yana bin tsarin da ya dace da mutuncin ɗan'adam da kuma kare ƙimar ɗan'adam tsayin daka. Netanyahu da abokansa mabiya siyasar kisan kiyashi ne,” ya ƙara da cewa.

'Ɓata suna'

A ranar Laraba Turkiyya ta yi watsi da "kalaman ɓatanci" da Netanyahu ya yi wa Erdogan kuma ya ce jami'an Isra'ila ba su da 'yancin yin magana game da dokar.

Isra'ila ta kai hare-hare ta sama da ta ƙasa a Zirin Gaza tun bayan harin ba-zata da ƙungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.

Akalla Falasdinawa 11,500 ne aka kashe tun daga lokacin, da suka hada da mata da yara sama da 7,800, yayin da sama da 29,200 suka jikkata, a cewar alkaluman baya-bayan nan daga hukumomin Falasdinu.

Dubban gine-gine, da suka hada da asibitoci da masallatai, da coci-coci aka lalata a hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama da kasa a kan yankin da aka yi wa ƙawanya.

Adadin wadanda suka mutu a Isra'ila, ya kai kusan 1,200, a cewar alkaluman hukuma

TRT World