Isra’ila ta sake nuna cewa ba ta da muradin kare fararen-hula ko girmama muhimman haƙƙoƙin ɗa’adam, in ji Daraktan Hukumar Sadarwa ta Turkiyya, Fahrettin Altun.
Altun ya bayyana hakan ne a shafinsa na X a daren Asabar inda yake magana a kan katse sadarwa da Isra'ila ta yi baki ɗaya a Gaza, yayin da ta fara kutsawa da kai hare-hare ta ƙasa cikin yankin a ranar Juma'a da daddare.
"Yanke hanyoyin sadarwa baki ɗaya da ya hada da waya da intanet a Zirin Gaza na nuna alamun matakin hare-hare na baya-bayan nan da sojojin Isra’ila ke ƙaddamarwa a kan Falasɗinawa," ya ce.
A yayin da rundunar sojin Isra’ila ke ci gaba da zafafa kai hare-hare a Zirin Gaza, wanda aka yi wa ƙawanya tun ranar 7 ga watan Oktoba, "ƙoƙarinta na katse da lalata hanyoyin sadarwa hari ne a kan haƙƙoƙin ɗan’adam da taɓa darajarsa.
"Matakin Isra’la na hana duk wata tashar sadarwa ta duniya aiki a Gaza da kuma katse Gazan daga sauran duniya, lamari ne da ɓaro-ɓaro ke nuna laifukan yaƙi. Wannan wani kokari ne na ɓoye mummunar gaskiyar kashe fararen hula da Isra’ila ke yi," a cewar Altun.
Kawar da kan Kasashen Yamma
Daraktan Sadarwan Turkiyyan ya kuma koka kan kawar da kan da kasashen Yamma suke yi a yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare, inda ya ce hakan ya sa sun kasance masu laifi.
"Babu wata hujja da za ta sa a rika kai hare-haren kan mai-uwa-da-wabi kan al’ummar Gaza da cin zarafin kowa da kowa.
"Dole wadanda suke kawar da kai yayin da Isra’ila ke kai hare-hare su sauya matsayarsu."
Ya jaddada cewa tarihi ba zai taba mantawa da wadannan ranaku na bakin ciki da takaici ba bisa rashin daukar matakan shawo kan wadannan hare-hare.
“Muna yin Allah wadai da kakkausar murya kan take hakki da ‘yancin al’ummar Gaza da sauran Falasdinawa da Isra’ila take ci gaba da yi. Manyan kasashen duniya da ke goyon bayan wannan ba su da bakin gaya wa wasu su bi doka daga yanzu," in ji Altun.