Shugaban ya yi kira ga ƙasashen duniya musamman ƙasashen Yamma da su "daina zura ido suna kallo Isra'ila na aikata munanan ayyuka tare da ɗaukar matakan daƙile ta. / Hoto: AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi Allah wadai da hare-haren da Isra'ila ke kaiwa a Lebanon, yana mai jaddada cewa waɗannan hare-haren sun tabbatar da damuwar Turkiyya game da burin Isra'ila na fadada rikici a yankin.

Da yake magana da manema labarai a ranar Asabar a Istanbul gabanin tafiyarsa zuwa New York, Erdogan ya ce Isra'ila na kai hare-hare kamar kungiyar ta'addanci.

"Da wannan harin (na na'urorin sadarwa a Lebanon), Isra'ila ta nuna ba ta da tausayin farar hula, za ta iya amfani da duk wata hanya domin cim ma mummunar manufarta," in ji shi.

Firaministan Isra'ila Benyamin Natanyahu da muƙarrabansa na amfani da duk wata hanyar tsokana domin aiwatar da akidarsu mai tsatsauran ra'ayi ta kafa ƙasar Yahudawa a Falasɗinu, in ji Erdogan.

'Ɗaukar mataki kan munanan ayyukan Isra'ila'

Yankin yanzu yana fuskantar "rikicin da ba za a iya bayyana shi ba," in ji shugaban na Turkiyya.

Shugaban ya yi kira ga ƙasashen duniya musamman ƙasashen Yamma da su "daina zura ido suna kallo Isra'ila na aikata munanan ayyuka tare da ɗaukar matakan daƙile ta."

Aƙalla mutum 37 aka kashe inda sama da mutum 3,250 daga ciki har da yara da mata suka jikkata a lokacin da "na'urorin sadarwa" suka fashe a Lebanon a ranakun Talata da Laraba.

Har yanzu Isra'ila ba ta ce komai dangane da fashewar ba.

TRT World