Hungary ta yaba wa Turkiyya kan yadda take wanzar da zaman lafiya a yankinsu

Hungary ta yaba wa Turkiyya kan yadda take wanzar da zaman lafiya a yankinsu

Shugabar kasar Hungary Katalin Novak ta kira Turkiyya da muhimmiyar kawa kuma abokiyar hulda mai muhimmanci
Shugabar kasar Hungary Katalin Novak ta kira Turkiyya da muhimmiyar kawa kuma abokiyar hulda mai muhimmanci. Hoto: AA

Shugabar kasar Hungary Katalin Novak ta kira Turkiyya da muhimmiyar kawa kuma abokiyar hulda mai muhimmanci, tana mai yaba wa rawar da take takawa wajen samar da zaman lafiya a yankinsu.

Novak ta fadi hakan ne a ranar Litinin a wani sako da ta wallafa a shafin sada zumunta na X, da a baya aka sani da Twitter, tana mai alakanta sakon da ganawarta da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, wanda ya ziyarci Hungary a ranar Lahadi.

"Turkiyya ba kawa da abokiyar hulda mai muhimmanci ba ce kawai ga Hungary, tana ma daya daga cikin kasashe kalilan da ke kokarin wanzar da zaman lafiya."

Erdogan ya kai wata ziyarar yini daya zuwa babban birnin Hungary, Budapest don halartar bikin ranar kasar da kuma Gasar 'Yan Tsere ta Duniya.

A shekarar 2013 ne dangantala tsakanin Turkiyya ta kara karfi bayan kaddamar da Cibiyar Hadin Kai. Kawancen ya samar da nasarori da dama a fannoni daban-daban a shekarun baya-bayan nan.

A watan Disambar nan mai zuwa, kasashen biyu sun shirya yin bikin murnar cika shekara 100 da fara huldar diflomasiyya.

AA