Altun ya kara jaddada buƙatar Turkiyya ta tsagaita wuta a rikicin da ake yi a Gaza. / Hoto: AA

Daraktan watsa labarai na Turkiyya a ranar Juma’a ya yi maraba da hukuncin na wucin-gadin da Kotun Ƙasa da Ƙasa ta yi dangane da Isra’ila.

“Kotun kasa da kasa ta yanke hukunci mai inganci a matsayin wani mataki mai karfi na kama Isra'ila kan laifukan yaki da ta aikata,” in ji Fahrettin Altun a shafinsa na X.

“Hukuncin na kotun ya kasance wata alama ta musamman da ta sha bamban da gazawa daban-daban da munafurcin wasu gwamnatocin ƙasashen yamma waɗanda suka yi shiru dangane da kisan ƙare dangin da Isra’ila ke yi,” kamar yadda ya ƙara da cewa.

Batun nasa na zuwa ne bayan kotun ICJ ta bayar da umarni ga Isra’ila ta “ɗauki duk wasu matakai a iya ƙarfinta” domin guje wa zubar da jini a Gaza. Haka kuma kotun ta buƙaci a saki duk wasu fursunonin yaƙi.

Ya ce Turkiyya ta yi maraba da matakin, yana mai bayyana fatan cewa zai share fagen yin hukunci ga Isra'ila da kuma yin adalci ga dubban Falasdinawa marasa laifi.

Ankara za ta goyi bayan duk wani yunƙuri na hukunta waɗanda ke da hannu wurin aikata laifukan da aka yi, in ji Altun.

Isra’ila ba ta fi ‘ƙarfin doka’ ba

“Muna kira da a fara tattaunawa don tabbatar da kasa mai cin gashin kanta ta Falasdinu. Mun yi imanin wannan ita ce hanya daya tilo don samun zaman lafiya mai dorewa,” in ji Altun.

Ya kara jaddada cewa, Turkiyya a karkashin jagorancin Shugaba Recep Tayyip Erdogan, za ta ci gaba da yin aiki tukuru don ganin an tsagaita wuta nan take.

“Shari'ar da ake ci gaba da yi a kotun ICJ za ta fargar Gwamnatocin Kasashen Yamma kan laifukan da Isra'ila ke yi wa Falasdinawa. Dole ne a daina mayar da Isra’ila shafaffiya da mai ta ɓangaren dokokin ƙasa da ƙasa,” in ji Altun.

Ya sake jaddada bukatar Turkiyya ta tsagaita wuta cikin gaggawa, da kai agajin gaggawa ba tare da tsaiko ba cikin Falasdinu, da kuma tattaunawa domin samar da kasashe biyu bisa iyakokin shekarar 1967.

A karshen watan Disamba ne kasar Afirka ta Kudu ta gabatar da koke dangane da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza a gaban kotun ICJ, inda ta bukaci da ta samar da matakan gaggawa na kawo karshen zubar da jini a Gaza, inda aka kashe Falasdinawa sama da 26,000 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.

TRT World