Hukumar Leƙen Asiri ta Turkiyya ta gudanar da wani aiki inda ta kawar da Abdulhamit Kapar, wanda ke iƙirarin shi jami'i ne na ƙungiyar ta'addanci ta PKK. / Hoto: AA

Hukumar Leƙen Asiri ta Turkiyya (MİT) ta kai wani samame domin kawar da Abdulhamit Kapar, ɗaya daga cikin jami'an ƙungiyar ta'addanci.

Abdulhamit Kapar, wanda aka fi sani da Tekin Guyi, ya kasance wani muhimmin jagora a ƙungiyar PKK/YPG da ke Syria.

Ya riƙe muhimman muƙamai, inda ya rinƙa kula da cibiyoyi da dama da ke ƙarƙashin YPG, wato ɓangaren soji na PKK/KCK da ke Syria. Waɗannan sun haɗa da ɓangaren kuɗi da ɓangaren jigilar kayayyaki da ɓangaren ƙere-ƙere da kuma wasu sassa da suka haɗa da ɓangaren fursuna da kuma gini ta ƙarƙashin ƙasa.

Tekin Guyi na daga cikin waɗanda Turkiyya ke nema ruwa-a-jallo kan kitsa wani hari da aka kai ofishin Jandarma na Sirnak/Uludere Tasdelen a ranar 15 ga watan 05 shekarar 1992, inda sojoji 26 suka yi shahada aka yi garkuwa da biyu.

Abdulhamit Kapar, wanda aka fi sani da Tekin Guyi, ya kasance wani babban jami'i a PKK/YPG da ke Syria.

Sakamakon ya shafe shekara 32 a ƙungiyar ta'addancin, ɗan ta'adda KAPAR ya yi ƙoƙarin ɓatar da sawu bayan ya rayu inda ya tsere bayan samamen da MIT ta kai a Derik a 2021.

Sai dai bai yi nasara ba. Sakamakon MIT na nan na nemansa tsawon lokaci kuma tana da yaƙinin cewa Tekin Guyi na a Qamishli inda a nan aka kashe shi.

AA