Hukumar ba da agaji ta Turkiyya ta kai kayan abinci na watan Ramadan ga ma'aikatar Waƙafi da Harkokin Addini ta Falasdinu da za a raba wa iyalai 1,000 da ke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira a garuruwa daban-daban na Falasɗinu.
Orhan Aydin, jami'in Hukumar Hadin Kan Turkiyya TIKA a Falasdinu, ya bayyana a ranar Alhamis cewa, za su ci gaba da bai wa al'ummar Falasdinu goyon baya a duk tsawon watan Ramadan.
Ya ce za su gudanar da ayyuka kamar rabon abinci da samar da kayan abinci da shirya buɗa-baki a sassa daban-daban na Falasdinu ciki har da Gaza.
A wani bangare na tallafin na watan Ramadan, hukumar agajin ta kuma ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira na Al Amari, wanda a baya-bayan nan ke fama da hare-hare, tare da raba kayan abinci ga iyalai mabuƙata.
Matsanancin ƙarancin abinci da ruwa mai tsafta da magunguna
Wahalhalun zamantakewa da tattalin arziki da suka samo asali daga manufofin mamayar da Isra'ila ta daɗe tana yi a Yammacin Gaɓar Kogin Jordan da ta mamaye da kuma yakin Gaza na ci gaba da tsananta.
Isra'ila ta ƙaƙaba wa yankin Falasdinawa wani takunkumin hana fita, lamarin da ya bar al'ummarta, musamman mazauna arewacin Gaza cikin barzanar faɗawa cikin matsananciyar yunwa.
Yaƙin Isra'ila ya jefa kashi 85 cikin 100 na al'ummar Gaza zuwa matsugunin cikin gida a cikin matsanancin ƙarancin abinci da ruwan sha mai tsafta, da kuma magunguna, yayin da aka lalata yawancin ababen more rayuwa a yankin, a cewar MDD.
Baya ga ƙaruwar rashin aikin yi da fatara bayan yaƙin, matsin lamba da hare-haren da ake kai wa garuruwa kamar Jenin da Tulkarm da Qalqilya da Tubas da Nablus da Ramallah, musamman ma sansanonin 'yan gudun hijira a wadannan garuruwa na ƙara ta'azzara.