Mai magana da yawun Jam'iyyar AK Omer Celik ya bayyana cewa hare-haren Isra'ila a kan Falasɗinawa "na ɗaya daga cikin manyan kisan kiyashin da aka shirya a zamanin yau."
Ya yi kalaman ne a wajen wani taron manema labarai a ranar Laraba, kwana ɗaya bayan da wani harin saman da ISra'ila ta kai Aisbitin Al Ahli Baptist da ke Gaza ya hallaka sama da mutum 500.
"Isra'ila ta ƙi bai wa Falasɗinawa damarsu ta rayuwa a ƙasarsu, tana kai musu hare-hare. Isra'ila ta gaya wa Falasɗinawa cewa su fita su bar gidajensu su koma kudanci, sai kuma ta kai musu hari a lokacin da suke tserewar," a cewar Celik.
"A ƙarshe, mutane sun gudu asibiti suna neman mafaka, suna tunanin cewa Isra'ila ba za ta iya cim musu a can ba, amma sai da Isra'ila ta kai musu hari a a sibitin ma," ya ƙara da cewa.
"Wannan ɗaya ne daga cikin manyan munanan abubuwa da muka gani a tarihin ɗan'adam.
Mai magana da yawun jam'iyyar ya jaddada cewa Turkiyya ta yi Allah wadai da "wannan mummunan rashin imanin da kakkausar murya."
Celik ya kuma cewa Turkiyya na tare da mutanen da ake zalinta da suka haɗa da yara da mata da tsofaffi da fararen hula a Falasɗinu.
"Wahalar da Falasɗinu ke sha tamu ce, kuma wannan rashi, rashi ne na duniya baki ɗaya."
‘Muguntar Isra’ila da ba a taɓa gani ba’
Turkiyya ta yi tir da Isra’ila kan harin da ta kai Asibitin Al Ahli Baptist da ke yankin Gaza na Falasɗinu, wanda ya kashe fiye da mutum 500.
“Kai hari kan asibitin da mata da yara da sauran fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba ke ciki shi ne mafi kololuwar cin zali da take darajar dan'adam na hare-haren Isra'ila,” in ji Erdogan a shafinsa na X.
“Ina kira ga dukkan mutanen duniya da su ɗauki matakin dakatar da “munanan hare-haren da ba a taɓa ganin irinsu ba” da Isra’ila ke kai wa Gaza,” ya ƙara da cewa.
Bidiyoyi sun nuna gawarwaki a barbaje a ƙasa a asibitin.
Dubban Falasɗiwa ne a asibitin a lokacin da aka kai masa harin.
Isra’ila ta ƙi ɗaukar alhakin kai harin, yayin da masu ruwa da tsaki a fadin duniya ke kira da gudanar da bincike mai zaman kansa don gano wanda ke da hannu a lamarin.
An kai harin ne a kwana na 12 da fara faɗa tsakanin Isra’ila da Hamas, inda ƙungiyoyin kare hakkin ɗan’adam da shugabannin duniya suke ta maganganu cewa kai hare-hare kan cibiyoyin lafiya da gidajen mutane da wuraren ibada, sun take dokokin yaƙi na ƙasa da ƙasa.