Shugaban Ƙasar Turkiyya Erdogan ya ce ba ya kallon Hamas a matsayin ƙungiyar ta'adda, yana mai cewa ƙungiya ce da ke kare yankunanta da Isra'ila ke mamaya.
"Daga 1947 har zuwa yau, Falasɗinu na ta rasa yankunanta a kowacce rana," in ji Erdogan a ranar Talata a yayin tattaunawa da NBC News da ke Amurka.
Da ɗan jarida Keir Simmons ya tambaye shi game da cewa "akwai masu sukar ka da Turkiyya, saboda bayar da mazauni ga Hamas, wadda Amurka ke kallo a matsayin ta 'yan ta'adda, kuma kana cewar kana yaƙi da ta'addanci," sai Erdogan ya ce "Tabbas muna yaƙi da ta'addanci."
"Amma ina ɗaya daga cikin shugabanni da suka san Hamas sosai. Ban taɓa kiran Hamas da sunan ƙungiyar ta'adda ba, kuma ba na kallon Hamas a matsayin ƙungiyar ta'adda."
Erdogan ya ce "Saboda Hamas ƙungiya ce ta gwagwarmaya da ke ƙoƙarin kare yankunanta. Saboda haka ta yaya zan kira ƙungiyar turjiya da ƙungiyar ta'addanci?"
Da yake amsa tambaya ga NBC a New York game da hare-haren 7 ga Oktoba da Hamas ta kai wa Isra'ila, Shugaban Ƙasar Turkiyya Erdogan ya ce ya kamata a yi duba ga dalilan da suka janyo hakan.
"Muna buƙatar sanin dalilan da suka janyo abin da ya faru a 7 ga Oktoba. Muna buƙatar fahimtarsu sosai. Kuma idan muka yi duba ga musabbabin lamarin da Falasɗinawa nawa ne suka yi shahada, nawa ne kuma aka kashe, za mu ga lamarin ya kai yanayi mummuna sosai," in ji shi.
Turkiyya na goyon bayan warware rikicin Isra'ila da Falasɗinu ta hanyar kafa ƙasashe biyu, ciki har da tabbatar da kafuwar 'yantacciyar ƙasar Falasɗinu kamar yadda iyakokin da aka shata a 1967 suke, kuma mai hedkwata a Birnin Ƙudus.
Isra'ila ta ci gaba da kai munanan hare-hare Gaza tun harin kan iyaka da Hamas ta kai a ranar 7 ga Oktoba, duk da matakin neman tsagaita wuta da Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ɗauka.
Sakamakon hare-haren na Isra'ila a Gaza kusan mutane 41,500, mafi yawan su mata da yara aka kashe tare da jikkata kimanin 96,100, kamar yadda hukumomin kiwon lafiya na yankin suka bayyana.
Hare-haren na Isra'ila sun tsugunar da kusan dukkan jama'ar yankin, a yayin da ake ci gaba da yi musu ƙawanya da ta janyo ƙarancin abinci, tsaftataccen ruwan sha da magunguna.
Isra'ila na fuskantar tuhuma a Kotun Ƙasa da Ƙasa kan aikata kisan kiyashi a Gaza.
Yunƙurin Ukraine na zama mamba a NATO
A yayin tattaunawar, da aka tambaye shi game da ra'ayin Ankara kan shigar Ukraine ƙawancen NATO, Erdogan ya ce Turkiyya za ta amince da dukkan matakan da sauran mambobin NATO suka ɗauka game da batun.
"Amurka ba ta son Ukraine ta zama mamba a NATO Hakazalika mambobin NATO da dama ba sa son hakan. Ya kamata mu kalli wannan gaskiya tare da ɗaukar mataki," in ji shugaban ƙasar na Turkiyya.
Erdogan ya kuma ce tambaya game da neman zama mamban NATO da Ukraine ke yi na bukatar duba na tsanaki, yana mai tsokaci da cewa "Idan muka muka kalli gaskiya lamarin, wadannan ba batutuwa ba ne da za a tunkara da kuzari."
"A lokacin da muke daukar matakai kan wadannan batutuwa, tabbas, muna kallon dukkan matsayin mambobin NATO sannan mu yanke hukunci," in ji shi yana mai cewar matakin karshe na Turkiyya zai zo bayan ta kalli matakin da sauran kasashe suka dauka.
"Ba a daukar wadannan matakai cikin gaggawa."
Ukraine ta bayyana karara tana son shiga kawancen NATO.
A yayin da har yanzu NATO ba ta karɓi Ukraine ba, ƙawancen ya ƙarfafa dangantakarsa da Kiev tun bayan fara yaƙi da Rasha a watan Fabrairun 2022.