"Duniya ba za ta ki yarda da cewa mafita ita ce a samar da 'yantacciyar kasar Falasdinu da ke da babban birni a Kudus.. / Hoto: AA

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce hadin kai da aiki tare tsakanin Ankara da Alkahira zai taimaka sosai wajen wanzar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da tsaro a yankinsu.

Da yake magana da 'yan jaridu a cikin jirgin sama a kan hanyarsa ta dawowa daga Masar bayan ziyarar kwana guda da ya kai kasar, Erdogan ya ce takwaransa na Masar Abdulfatah Al Sisi zai ziyarci Turkiyya a watan Afrilu ko Mayu.

"Muna da niyyar karfafa hadin kan mu da Masar don kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza, a kuma samar da zaman lafiya mai ɗorewa da zai biya bukatar Falasdinawa," in ji shugaban na Turkiyya.

Sai dai kuma, ya soki Amurka kan matsayinta game da rikicin da Isra'ila ta kashe sama da mutum 28,000 tun 7 ga Oktoba.

Ya ce "Abun takaici kiran samar da zaman lafiya a Gaza bai karɓu ba saboda nuna halin ko in kula daga ɓangaren Amurka."

Erdogan ya kuma ce hari kan Gaza, da ake ci gaba da yi tun 7 ga Oktoba bayan harin da Hamas ta kai, na nuni da tsagwaron 'rashin tunani irin na Isra'ila', kuma na nufi da ba za a iya fatali da batun tsaron jama'ar yankin ba.

Shugaban Turkiyya ya kara da cewa "Duniya ba za ta ki yarda da cewa mafita ita ce a samar da 'yantacciyar kasar Falasdinu da ke da babban birni a Kudus, kamar yadda aka shata iyakoki a 1967."

Ya tambayi cewa "Shin tilastawa fararen hula su bar wani yanki kafin kai harin bam wani bangare ne na ayyukan jin kai, dokokin yaki, dokokin kasa da kasa, hakkokin dan adam?"

Turkiyya ta samu "sakamakon a zo a gani wajen samar da zaman lafiya a yakin Yukren da Rasha".

A yakin da ake yi tsakanin Rasha da Yukren, Erdogan ya ce Ankara ta samu "sakamakon a zo a gani wajen samar da zaman lafiya a yakin Yukren da Rasha" kuma za ta iya ci gaba da yin haka.

"Ya zuwa yanzu, mun samar da sakamako mai kyau wajen samar da zaman lafiya a yakin Rasha-Yukren. An samu ci gaba masu muhimmanci da yawa, tun daga musayar fursunoni, zuwa ga samar da hanyar safarar hatsi," in ji Erdogan.

"Har ta kai ga mun hada bangarori daban-daban waje guda a lokuta da dama a Turkiyya. Za mu iya sake yin hakan, mu bude kofar samar da zaman lafiya, tsarin da ba zai samu katsalandan daga kasashen waje ba."

Erdogan ya ce a tattaunawar da Turkiyya ta yi da shugaban Rasha Vladimir Putin da na Yukren Vladimir Zelensky, Turkiyya na ci gaba da kokarinta don ganin an samar da daidaito.

Ya jaddada cewa Ankara ba za ta daina neman a zauna lafiya ba, yana mai cewa "Za mu ci gaba da yin duk mai yiwuwa don ganin an samar da zaman lafiya."

Alaka da Amurka

Bangarori da dama na kallon amincewar da Amurka ta yi na a sayarwa da Turkiyya jiragen yaki samfurin F-16 bayan majalisar dokokin kasar ta amince da Sweden ta shiga NATO, wani yunkuri ne na sake karfafa alakar da ke tsakanin ƙawaye a NATO.

Shugaban na Turkiyya ya ce akwai "Cigaba mai kyau" kan alakar Ankara da Washington.

Ya kara da cewa a yanzu majalisar dokokin Amurka na yi wa Turkiyya kyakkayawan kallo.

Ya ce "Za mu iya cewa mu da Amurka mun cimma matsaya kan wasu batutuwa da muke aiki tare a kai."

"Babu wani yanayi mara kyau; tabbas, akwai ci gaba mai kyau da ake iya gani."

Turkiyya ta samu cigaba sosai tare da Erbil wajen yaki da ta'addanci.

Turkiyya na ci gaba da kai farmakai a kan iyakokinta don yaki da 'yan ta'addar PKK a arewacin Siriya da Iraki.

Shugaban kasar Turkiyya ya kuma cewa kasarsa ta samu cigaba a hadin ka da take yi da Erbil wajen yaki da ta'addanci, amma duk da gargadin da suka yi, gwamnatin Sulaimaniya na ci gaba da bayar da kariya ga 'yan ta'addar PKK/YPG.

A hare-haren ta'addanci da PKK ta ɗauki shekara 35 tana kaiwa a Turkiyya, Turkiyyar da Amurka da Ingila da Tarayyar Turai sun bayyanata a matsayin ta ta'addanci, ta yi ajalin sama da mutum 40,000 da suka haɗa da mata da yara ƙanana da jarirai.

YPG/PYD ne reshen PKK a Siriya.

TRT World