Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta miƙa saƙon jajenta ga Turkiyya sakamakon wata mummunar gobara da ta faru a lardin Bolu da ke ƙasar inda akalla mutum 76 suka rasu, wasu 51 kuma suka samu jikkata.
Ƙasar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar.
“Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na mika sakon ta'aziyyarta tare da nuna goyon bayanta ga Jamhuriyar Turkiyya kan mutanen da suka mutu a gobarar da ta tashi a wani otel a lardin Bolu, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama da kuma jikkata,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
“Ma'aikatar harkokin wajen kasar na bayyana jajenta ga gwamnati da al'ummar kasar Turkiyya, da kuma iyalan waɗanda wannan bala'i ya rutsa da su, tare da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata,” kamar yadda ma’aikatar ta ƙara da cewa.