Kungiyar ta'addanci ta PKK/YPG mai samun goyon bayan Amurka da kawayenta na ci gaba da mayar da yara sojojin yaki a arewacin Syria da arewacin Iraki, a cewar Ma'aikatar Tsaro ta gwamnatin rikon kwarya ta Syria.
An sace yaran Larabawa da Turkmenistan da dama a gabashin Syria inda aka tursasa su shiga kungiyar ta'addanci ta PKK/YPG, wacce Amurka ke goya wa baya, tare da kawayenta irin su SDF da Revolutionary Youth, a cewar rahoton.
Kungiyar ta'addancin da kungiyoyin da suke da alaka da ita sun dauki yara da dama aiki tare da kai su arewacin iraki don shiga kungiyar ta PKK.
Da yake ba da alkaluman Majalisar Dinkin Duniya, ma'aikatar ta ce kungiyar ta'addanci ta PKK/YPG da Amurka ke goyon baya da kawayenta, suna da yara sojojin yaki fiye da 700. Yawan yara kanana sosai daga cikinsu ya kai 1,696 a shekarar 2022.
Gwamnatin rikon kwarya ta Syria ta haramta mayar da yara sojojin yaki
A watan Mayun shekarar 2020, Ma'aikatar Tsaro ta Gwamnatin Rikon Kwarya ta Syria wacce majalisa ta amince da ita, ta fitar da wata doka da ta haramta mayar da yara sojojin yaki a rundunar sojin Syria (SNA).
Dokar ta haramta wa SNA da shugabanninta saka yara a duk wani abu da ya shafi harkar soji ko ta fararen hula, kamar yadda dokokin kasa da kasa suka haramta.
Take dokokin wadannan haramce-haramce za su iya sa wa a tuhumi wanda ya aikata da tuumar miyagun laifuka, a cewar ma'aikatar.
'Rundunar sojin da ke samun horon shari'ar kasa da kasa'
Rundunar SNA tana tabbatar da wasu matakai na sauya dabi'u, inda rundunoni da dama suke sanya hannu kan yarjejeniyar ayyukan da suka shafi tsarin shari'un jinkai na kasa da kasa. Ana yawan yi wa dakarun sojin horo sosai.
Daga tsakanin watan Agustan 2021 zuwa Janairun 2023 rundunar SNA ta shirya kwas-kwasai 85 na shari'ar hakkokin dan adam, inda wata kungiya mai suna Geneva Call ta gabatar. A wannan lokacin, jami'ai 1480 ne suka amfana da wannan hron, a cewar ma'aikatar.
Ma'aikatar ta ce a wannan dan tsakanin, SNA ta yi hadin gwiwa da kungiyoyi irin su Afaq da Ward Al Balad da Benevolent Seed Humanitarian da Human Rights Guards Organisation da kuma ORSAM a kokarinta na bin tsarin dokokin jinkai da mutunta dan adam na kasa da kasa.
A kalla jami'an sojin Syria 15,000 ne a mukamai daban-daban ne aka yi wa horo sakamakon hadin gwiwar da take yi.