Bayan shafe kwanaki 54, an sada wata jaririya wacce aka ceto daga baraguzan ginin da girgizar kasa ta auku a kudancin Turkiyya da mahaifiyarta.
An ceto jaririyar mai suna Vetin Begdas a lardin Hatay, sa’o’i 128 bayan girgizar kasa da ta auku a watan Fabrairu.
Daga nan aka kai ta wani asibiti a Ankara babban birnin kasar domin ba ta kulawa.
Jami'an kiwon lafiya a asibitin sun rada mata suna da ‘’Yar baiwa’’ wato Gizem a harshen Turkanci.
A ranar Asabar ne Ministar kula da walwalar jama’a da iyali Derya Yanik ta sada jaririyar da mahaifiyarta mai suna Yasemin Begdas a lardin Adana.
Hakan ya faru ne bayan gwajin kwayoyin halittar da aka yi wanda ya tabbatar da dangantakar da ke tsakanin uwar da jaririyar.
Mahaifin jaririyar dai da yayyenta maza biyu sun mutu sakamokon girgizar kasa da ta rutsa da su wadda kuma ta yi sanadin mutuwar sama da mutum 50,000.
''Jaririyar yar’ baiwa ce, ta yi matukar shiga zukatanmu, duba da yadda ta tsira da kuma ba ta samu wata illa ga lafiyarta ba," in ji Yanik.
Ta kara da cewa ‘’Yar’ baiwa yanzu 'yarmu ce, kuma ma’aikatarmu za ta ci gaba da tallafa mata."