Turkiyya ta yi Allah-wadai da yakin kisan ƙare dangi da Isra'ila ta ke yawan yi kan yankunan da aka killace a Gaza, lamarin da ya janyo cikas ga yunƙurin Ankara da sauran masu shiga tsakani na neman a tsagaita wuta. / Hoto: AA 

Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya tattauna ta wayar tarho da shugaban ɓangaren siyasa na ƙungiyar Hamas Ismail Haniyeh, inda suka mayar da hankali kan mummunan yanayin da ake ciki a Gaza wadda Isra'ila ta yi ƙawanya.

Ɓangarorin biyu sun tattauna ne a ranar Talata game da halin da ake ciki na jinƙai a Gaza, yanayin da ya tsananta sakamakon yakin Tel Aviv na kisan ƙare-dangi.

Kazalika, sun tattauna kan matsalar yunwa da cututtuka da ke ta'azzara musamman a arewacin Gaza.

Shugabannin biyu sun kuma taɓo batun sabuwar tattaunawar tsagaita wuta da Isra'ila ke jan-ƙafa a kai.

Yunƙurin Turkiyya ga Falasɗinu

Tun bayan fara kisan kiyashi da Isra'ila ke yi a Gaza, Turkiyya ke amfani da dukkan hanyoyinta wajen ganin an tsagaita wuta a yankin da aka killace tare da aika kayan agaji ga Falasɗinawa da aka yi wa ƙawanya.

A safiyar ranar Talata ne, shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa matsayar Ankara ba za ta canja ba kan Tel Aviv ''muddin Isra'ila ta ci gaba da kisan gilla da mamaya da kuma aiwatar da manufofinta na kisan ƙare-dangi a Gaza da sauran yankunan Falasɗinawa.''

A makon da ya gabata ne, Erdogan ya yi amfani da shafin intanet na NATO wajen yin Allah wadai da yaƙin Isra'ila a Gaza, inda ya buƙaci ƙasashen duniya su matsa wa Isra’ila lamba wajen ganin ta amince da batun tsagaita wuta.

Turkiyya ta yi Allah wadai da kisan ƙare-dangi da Isra'ila ke ci gaba da yi a yankunan da ta killace a Gaza, lamarin da ya janyo cikas ga yunƙurin Ankara - da sauran masu shiga tsakani -wajen neman a tsagaita wuta

Ankara dai na ci gaba da aika kayan agaji zuwa ga Falasdinawa da aka yi wa kawanya a Gaza, wadanda ke cikin mawuyacin hali sakamakon yakin Isra'ila da ya haifar da ƙarancin kayayyakin amfani da suka ruwa da abinci da wutar lantarki da kuma magunguna.

TRT World