A kisan kiyashin Gaza, gwamnatocin Yammacin duniya ba su tabuka abin a zo a gani ba, sun zubar da girmansu wajen kare Isra'ila," in ji shugaba Erdogan. / Hoto: AA

Ta'annatin da Isra'ila ke aikatawa a yankin Gaza na Falasɗinu ya bayar da gudunmawa wajen fitowa fili a fahimci yadda 'yan koren Isra'ila ke da iko kan manyan jami'o'in duniya, in ji shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

"Mun shaida irin wannan abin kunyar inda 'yan sanda suka dinga musguna wa ɗaliban da suka ce 'ana aikata kisan kiyashi a Gaza', shugaba Erdogan ya bayyana haka a ranar Talata a yayin taron ɗabuwar shekarar karatu ta 2024/2025 a Ankara.

Ya kuma ja hankali kan yadda aka tursasa wa shugabannin jami'o'i da suka bayar da damar yin zanga-zangar adawa da kisan Falasɗinawa yin murabus, aka azabtar da su tare da titsiye su a gaban majalisar dokokin a Amurka.

Ya jaddada cewa "Babu wani suka ko bayyana ra'ayi game da Falasɗinawa aka yarda da shi. Ya zama babu tantamar cewa 'yan koren Isra'ila ne ke riƙe da iko da manyan jami'o'in duniya inda suke fakewa da bayar da tallafin kuɗaɗe."

Shugaban na Turkiyya ya kuma soki gwamnatocin ƙasashen Yammacin duniya bisa gazawa wajen kawo ƙarshen kisan kiyashi a Gaza tsawon shekara guda, yana mai cewa sun zubar da ƙimarsu "a ƙoƙarin da suke yi na kare Isra'ila".

Yaƙi da dukkan 'yan'adam

Da take ci gaba da saɓa wa matakin da Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ɗauka na kiran da a tsagaita wuta a Gaza, Isra'ila na ci gaba kai munanan hare-hare Gaza, tana mai fakewa da harin da ƙungiyar tirjiya ta Falasɗinawa Hamas ta kai mata a ranar 7 ga Oktoban 2023.

Hare-Haren na Isra'ila sun tsugunar da kusan dukkan jama'ar yankin da ci gaba d fuskantar mamayar da ta janyo karancin abinci, tsaftataccen ruwan sha, da magunguna.

Ƙoƙarin shiga tsakani da Amurka, Masar da Qatar ke jagoranta don a tsagaita wuta a Gaza da yin musayar fursunoni tsakanin Hamas da Isra'ila ya ci tura saboda yadda Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dakatar da yaƙin.

Yaki na tsawon shekara guda da Tel Aviv ke yi a Gaza ya yi ajalin mutane 42,000. Isra'ila na fuskantar tuhumar aikata kisan kiyashi a Kotun Kasa da Kasa saboda ta'annatin da ta aikata a yankin, da ke da Falasdinawa sama da miliyan biyu.

A gefe guda, hare-haren Isra'ila a Lebanon tun daga 2023 zuwa yau sun yi sanadiyar mutuwar sama da mutum 2,000 inda aka raba wasu milayan 1.2 da matsugunansu.

Muna amfani da ka’idojin yanar gizo. Muna son ku san cewa idan kuka ci gaba da amfani da wannan shafin, kun amince da wadannan ka’idojin.Ka’idoji
Na amince