Erdogan ya kai ziyarar aiki Spain domin halartar taron gwamnatocin kasashen biyu karo na takwas. /Photo: AA

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jinjina wa firaministan kasar Spain Pedro Sanchez kan matakin da ya ɗauka kan rikicin da ke ci gaba da faruwa a Gaza.

"Ina taya abokina, Firaiminista Pedro Sanchez murna, bisa matsayarsa a kan Gaza, a madadin kaina da al'ummata," in ji Erdogan a ranar Alhamis a wani jawabi da ya yi a wani taron kasuwanci a Madrid babban birnin Spain, inda ya kara da cewa Sanchez "ya kasance a cikin zukatan 'yan'uwanmu Falasdinawa."

Erdogan ya kai ziyarar aiki Spain domin halartar taron gwamnatocin kasashen biyu karo na takwas.

Shugaban na Turkiyya ya ƙara da cewa a wajen taron, wanda Sanchez ma ya halarta, cewa "kisan kiyashin da ake yi a Gaza tsawon kwanaki 250 yana cutar da kowa da kowa."

Har ila yau ya dauki manufar abin da ya kira halin da kasar Isra'ila ke ciki, yana mai cewa gwamnatin kasar karkashin jagorancin Firaiminista Benjamin Netanyahu, "tana amsa kiran tsagaita wuta ta hanyar zubar da jini."

Erdogan ya ce "Ba wata ƙasa da ta san ya kamata da za ta amince da hakan."

Fiye da Falasdinawa 37,200 aka kashe tun a Gaza, yawancinsu mata da kananan yara, yayin da wasu fiye da 84,900 suka jikkata, a cewar hukumomin lafiya na yankin.

Watanni takwas kenan da fara yakin Isra'ila, inda yankunan Gaza da dama suka zama kufai a cikin yanayi na saka takunkumin shigar da abinci da ruwan sha da magunguna.

Bunkasa hukumar kwastam

Shugaban na Turkiyya ya kuma taɓo batun alaƙar Turkiyya da Tarayyar Turai.

"Rashin sabunta Hukumar Kwastam da tsauraran aikace-aikacen biza da aka sanya wa 'yan kasuwarmu ya hana yin amfani da damarmu tare da kungiyar," in ji shi.

Dangane da alaƙar da ke tsakanin kasashen biyu, firaministan Spain ya bayyana cewa, Turkiyya na daya daga cikin "manyan abokan tattalin arzikin kasar Spain".

Pedro Sanchez ya bayyana ya shai da wa Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da wakilai daga 'yan kasuwar Spain da na Turkiyya da suka halarci taron cewa, "manyan damarmaki" na ci gaba da bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

'Spain ce babbar ƙawar Turkiyya a Turai'

"Mun san cewa duk da hawa da sauka, tushen tsarin Turkiyya zai ci gaba da bunƙasa cikin nauyin tattalin arziki da kuma muhimmancin siyasa a cikin shekaru masu zuwa," in ji shi.

Firaiministan ya yaba da "jajirtattun" matakai na gwamnatin Turkiyya da kuma "tsarin tattalin arziki mai tsauri" wanda ke jagorantar farfado da tattalin arzikinta. Ya kuma miƙa godiyarsa ga gwamnatin Turkiyya bisa yadda take ta sauraron damuwar kamfanonin kasar Spain.

"A lokacin da wasu suke shakka, mu mun ci gaba da gaskatawa. Ya kara da cewa, "lokacin da wasu ke janye hannun jari daga Turkiyya, muna ƙara ba da goyon bayanmu."

"Spain ita ce babbar kawar Turkiyya a Turai. Ina tsammanin wannan magana ce da ba ta buƙatar cece-kuce, "in ji Sanchez, yana mai nuni da saka hannun jarin Spain da sha'awar kasuwanci a kasar.

Kamar yadda Sanchez ya bayyana, muhimmiyar dangantakar Turkiyya da Asiya, Turai, da Afirka suna da matukar dacewa ga matsayin Spain a cikin EU da kuma kusanci da Latin Amurka.

Haɗin kai tsakanin kasuwancin mutanen Spain da Turkiyya

Ya kira taron na ranar Alhamis a Madrid da kuma manufofin gwamnatin Turkiyya "manyan damarmaki" don inganta ƙawance tsakanin 'yan kasuwa na Spain da na Turkiyya da kuma kasuwannin wasu ƙasashen.

Spain da kasuwancinta suna buƙatar Turkiyya mai ƙarfi da wadata,” in ji Sanchez.

A gun taron, Sanchez ya sanar da wasu sabbin yarjejeniyoyin da suka shafi kasuwanci guda biyar da nufin share fagen kara hadin gwiwa a fannin kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

TRT World