Shugaba Erdogan ya bayyana fatan cewa wa'adi na  biyu na Trump a matsayin shugaban kasar Amurka zai bayar da dama karfafa dangantakar Ankara da Washington tare da samar da sabbin damarmaki don magance manyan kalubalen duniya. / Photo: AA Archive

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya taya murna ga Donald Trump bis anasarar lashe zaben shugaban kasar Amurka bayan fafatawa mai zafi.

"Ina taya abokina Donald Trump murna bisa sake zabarsa a matsayin Shugaban Kasar Amurka bayan zazzafar fafatawa a zabe," in ji Erdogan a sakon da ya fitar ta shafin X.

A sakon da ya fitar, Shugaba Erdogan ya bayyana fatan cewa wa'adi na biyu na Trump a matsayin shugaban kasar Amurka zai bayar da dama karfafa dangantakar Ankara da Washington tare da samar da sabbin damarmaki don magance manyan kalubalen duniya da suka hada da batun Falasdinu da rikicin Rasha da Ukraine.

Shugaban na Turkiyya ya karfafa cewa a yayin da Trump ke dawo wa mulkin Amurka, zabin jama'ar Amurka na nuni ga farawar wani sabon shafi da ke dauke da muhimmin cigaba wajen warware rikice-rikicen yankin da ma a duniya baki daya.

Ya yi karin haske da cewar karfafa alakar Turkiyya-Amurka zai zama abu mai muhimmanci, kasancewar kasashen biyu mambobin NATO da ke da manufofi iri guda a yankuna daban-daban.

A sakon nasa, Erdogan ya yi fatan za a sabon sabon yunkurin kasa da kasa wajen tabbatar da tsari na adalci a duniya, yana mai nuni ga bukatar daukar matakin bai daya wajen warware matsalolin da suka dade suna addabar duniya.

Ya bayyana cewa duniya na bukatar babban hadin kai don kawo karshen yaƙe-yaƙe da rikice-rikice, ciki har da goyon bayan manufofin Falasdinawa da bukatar gaggawa ta zaman lafiya a Gabashin Turai, inda yaki tsakanin Rasha da Ukraine ke ci gaba da ruguza rayuwar mutane da tattalin arziki.

"Ina fatan wadannan zabuka za su kawo yalwa ga abokai kuma ƙawaye Amurka da dukkan 'yan adam," in ji shugaba Erdogan.

TRT World