Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya karbi baƙuncin takwaransa na Azabaijan Ilham Aliyev a birnin Ankara inda suka tattauna kan hanyoyin inganta huldar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma kara hadin gwiwa tsakanin su.
"A karshen mamayar da aka yi a Karabakh, wata gagarumar dama ta samun zaman lafiya mai ɗorewa a yankinmu ta samu, a cewar bayanan Shugaba Erdogan ga manema labarai bayan ganawar.
A yayin da yake sukar matakin da Majalisar Dokokin Turai PACE ta yanke na ƙin amincewa da wakilcin tawagar Azarbaijan, Erdogan ya ce: "Za mu ci gaba da nuna goyon bayanmu da kuma shirye-shiryenmu kan Azarbaijan har sai matakin ya rushe."
Muhimmancin ƙawancen Turkiyya da Azerbaijan
A yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka yi bayan ganawarsu ta ƙut da ƙut, Aliyev ya ce ƙawancen da ke tsakanin Turkiyya da Azabaijan ba wai kawai iyakar yankin ya shafa ba har ma da yankin Eurasia.
A yammacin ranar Lahadi ne Aliyev ya isa kasar Turkiyya a wata ziyarar aiki ta kwana biyu bisa gayyatar da shugaban kasar ya yi masa, wanda ke zama ziyararsa ta farko zuwa kasashen waje tun bayan sake zaɓensa a farkon watan nan.
Bangarorin biyu sun tattauna dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma ci gaban yankin da na duniya a halin yanzu, a cewar wata sanarwa da ma'aikatar yada labarai ta Turkiyya ta fitar a ranar Lahadi.
Haduwar manyan jami'an
Manyan jami'an tattalin arzikin Turkiyya biyu da shugaban tattalin arzikin Azabaijan sun gana domin tattauna dangantakar tattalin arziki da kasuwanci tsakanin kasashensu.
Ministan kasuwancin Turkiyya Omer Bolat da Ministan Baitulmali da Kudin kasar Mehmet Simsek da kuma Ministan Tattalin Arzikin Azabaijan Mikayil Cabbarov sun gana a Ankara babban birnin Turkiyya.
Cabbarov ya yi wa shugaban kasar Azabaijan Ilham Aliyev rakiya ne a ziyarar da ya kai kasar Turkiyya.
Sun gudanar da taron samar da shawarwari kan makomar dangantakar tattalin arzikin Turkiyya da Azabaijan, inda suka tattauna batutuwa daban-daban masu muhimmanci da suka hada da makamashi da kasuwanci da kuma hanyoyin zuba jari, in ji Bolat.
"Mun amince da ƙara zurfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashenmu biyu tare da aiwatar da wasu ayyukan hadin gwiwa," in ji shi.
"Wannan taro zai ba da gagarumar gudunmawa wajen kara karfafa alaka tsakanin kasashenmu."