Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya nuna rashin amincewa kan kalaman shugaban Amurka Joe Biden da ya nemi kasashen duniya su bai wa Ukraine goyon baya a daidai lokacin da Rasha ke ci gaba da kutsawa kasar, sannan ya yi watsi da sukar da yake sha na goyon bayan Isra'ila da yake yi a yaƙin da take yi a Zirin Gaza.
Sanarwar musamman da aka raba ga Newsweek ta ce, Erdogan da ke halartar taron NATO a Washington DC, ya soki Ƙasashen Yammacin Duniya saboda halayyar da suke nuna wa game da rikicin Ukraine da Gaza.
Erdogan ya ce manyan Ƙasashen Yamma na daukar matakai masu hatsari game da rikicin biyu, wanda ya yi gargadi da cewar zai iya yaduwa zuwa arangama tsakanin yankuna.
"Mafita ita ce zaman lafiyar da aka samar ta hanyar tattaunawa"
Game da Ukraine, wanda shi ne babban batun taruwar NATO, Erdogan ya sake jaddada matsayinsa na adawa da shiga yaƙin, duk da kiran da Biden ya yi na NATO ta hada kai ta kalubalanci Rasha.
"Mafitar ba ci gaba da zubar da jini da shan wahala ba ne, ana son dauwamammen zaman lafiya ne da za a samu ta hanyar tattaunawa," in ji Erdogan ga Newsweek.
Ya soki dabaru da ayyukan ƙawayensu na Yammacin Duniya, yana mai cewa "Halayyar wasu daga cikin ƙawayenmu na Yamma ga Rasha na ƙara rura wutar rikicin ne.
"Wannan ya janyo cutarwa maimakon amfanarwa ga Ukraine. Sabanin haka, muna tattaunawa da dukkan bangarorin da ke rikici da juna, a kokarin ganin sun kusanci zaman lafiya."