Erdogan ya  bayyana gamsuwa game da kyautatuwar alaƙar Turkiyya da Amurka

Erdogan ya  bayyana gamsuwa game da kyautatuwar alaƙar Turkiyya da Amurka

Shugaban Turkiyya ya ce ana ci gaba da samun bambancin ra'ayi da gwamnatin Amurka game da wasu batutuwan tsaro.
Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gana da wasu kungiyoyin Amurka a birnin New York. / Hoto: AA

Shugaban Kasar Turkiyya ya yaba yadda a baya-bayan nan aka samu kyautatuwa da ingantar alakarsu da Amurka.

"Mun ji dadin kyautatuwar alakar Turkiyya da Amurka a baya-bayan nan," Shugaba Erdogan ya fada wa wakilan wasu kungiyoyi masu zaman kansu na Amurka da ya gana da su a birnin New York a ranar Lahadi.

Erdogan ya isa birnin New York ranar Asabar kuma zai yi jawabi ga Taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 a ranar Talata.

"Ana ci gaba da samun bambancin ra'ayi da gwamnatin Amurka kan wasu batutuwa da suka shafi tsaron kasarmu," in ji shugaban na Turkiyya.

Tun da jima wa Turkiyya ke korafi kan yadda Amurka ke aiki tare da PKK da rassanta da sunan yaki da 'yan ta'addar Daesh. Jami'an Turkiyya sun ce amfani da dan ta'adda a yaki wani dan ta'addar abu ne marar hikima.

Da yake tabo alakar tattalin arziki, Erdogan ya ce jarin kasuwancin da ke tsakaninsu da Amurka ya haura dala biliyan $30 a 2023.

Ya kara da cewa "Mun yi amanna cewa za mu iya kara wannan adadi zuwa dala biliyan $100."

Game da zaben shugaban kasar Amurka da za a gudanar a ranar 5 ga Nuwamban bana, Erdogan ya ce Turkiyya na sanya idanu sau da kafa kan zaben da za a fafata tsakanin Mataimakiyar Shugaban Kasar Amurka Kamala Harris da tsohon shugaban kasa Donald Trump.

Ya kara da cewa "Ba tare da duba ga waye zai zama shugaban kasa ba, fahimtarmu da tattaunarmu mai muhimmanci da Amurka ba z ata sauya ba."

TRT World