Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da firaministan Pakistan Shehbaz Sharif sun jaddada aniyarsu ta karfafa alakar kasashen biyu da fadada hadin gwiwar tattalin arziki.
Shugaban na Turkiyya ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa a ranar Alhamis a birnin Islamabad, inda ya ce, "Tare da Firaminista, mun jaddada muhimmancin haɗin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu, tare da ƙarfafa masu zuba jari na Turkiyya su fadada ayyukansu a Pakistan.
"(Ta hanyar dandalin kasuwanci na Turkiye-Pakistan) Muna karfafa masu zuba jarinmu, wadanda su ne ginshikin hadin gwiwar tattalin arziki, da su kara yin ayyuka a Pakistan," in ji shi.
Shugaban Erdogan ya isa Pakistan a ranar Laraba, a ziyarar da Islamabad ta ce "za ta taimaka wajen kara zurfafa 'yan’uwantaka da inganta hadin gwiwar bangarori daban-daban a tsakanin kasashen biyu."
Tawagar jami'an Pakistan da suka hada da Shugaba Asif Ali Zardari da firaminista Shehbaz Sharif sun tarbi Erdogan da yammacin jiya Laraba a tashar jirgin saman Nur Khan da ke Islamabad babban birnin kasar.
Shugaban na Turkiyya yana tare da wata tawaga da suka hada da uwargidansa Emine Erdogan, da ministan harkokin wajen kasar Hakan Fidan, da ministan tsaro Yasar Guler, da daraktan sadarwa Fahrettin Altun.
A yau alhamis ne = Erdogan ya gana da Firaminista Sharif, kuma ya halarci taro karo na 7 na majalisar koli ta manyan tsare-tsaren hadin gwiwa ta HLSCC tsakanin kasashen biyu.
Ma'aikatar harkokin wajen Pakistan a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce "A karshen zaman, ana sa ran za a rattaba hannu kan wata sanarwar hadin gwiwa da wasu muhimman yarjejeniyoyi.
Shugabannin biyu za su kuma yi jawabi a wani taron manema labarai na hadin gwiwa."
"Pakistan da Turkiyya na da alaka mai cike da tarihi. Ziyarar shugaban kasar Turkiyya da kuma gudanar da taro karo na 7 na HLSCC zai taimaka wajen kara zurfafa alakar 'yan’uwantaka da inganta hadin gwiwar bangarori daban-daban a tsakanin kasashen biyu."
Batutuwan kasashen biyu da na yanki Ana kuma sa ran Erdogan zai halarci taron kasuwanci na Turkiyya da Pakistan tare da ganawa da Zardari a Fadar Shugaban Ƙasa.
Cibiyar HLSCC shi ne dandalin yanke shawara mafi kololuwa, wanda ke ba da jagoranci bisa dabaru don kara karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Ma'aikatar harkokin wajen Pakistan ta bayyana cewa, akwai wasu kwamitoci na dindindin na hadin gwiwa a karkashin HLSCC, wadanda suka shafi bangarorin da suka hada da kasuwanci da zuba jari da harkokin banki da kudi da al'adu da yawon bude ido da makamashi da tsaro da aikin gona da sufuri da sadarwa da fasaha da kiwon lafiya da kimiyya da ilimi, in ji ma'aikatar harkokin wajen Pakistan.
Karfin goyon bayan da Ankara ke bai wa Falasdinu da Kashmir ya yi daidai da manufofin Pakistan na ƙetare. Ana sa ran shugabannin bangarorin biyu kuma za su tattauna batutuwan yankin da kuma yakin kisan kare dangi da Isra'ila ke yi a Gaza.