Emine Erdogan da shugaban MDD sun tattauna kan sauyin yanayi da shirinta na Zero Waste

Emine Erdogan da shugaban MDD sun tattauna kan sauyin yanayi da shirinta na Zero Waste

A taron COP29,  Azabaijan na shirin jagorantar zaman tattauna kan shirin sauyin yanayi tare da haɗin gwiwar Turkiyya.
Uwargidan shugaban Turkiyya na birnin New York domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 tare da maigidanta Recep Tayyip Erdogan. / Hoto: AA  

Uwargidan shugaban ƙasar Turkiyya Emine Erdoğan ta gana da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Antonio Guterre a hedkwatar Majalisar da ke birnin New York, inda suka tattauna kan shirinta na sarrafa shara a duniya wato 'Zero Watse' da kuma batutuwan da suka shafi sauyin yanayi, kamar yadda wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ta bayyana.

A matsayinta na shugabar kwamitin ba da shawarwari kan shirin Zero Watse a MDD, Erdogan ta bayyana ayyukan da hukumar ke yi na ƙudurin samar da ci gaba mai ɗorewa a yayin ganawarta da Guterres a ranar Talata, inda ta jaddada muhimmancin tallafin da MDD ke bayarwa.

Kazalika Emine Erdogan ta bayyana irin haɗin gwiwar Turkiyya da Azabaijan a shirye-shiryen taron sauyin yanayi na MDD karo na 29 (COP29), wanda za a gudanar a Baku a cikin watan Nuwamba.

Daya daga cikin ranakun jigo a COP29 ana sa ran za a mai da hankali kan "Zero Waste," tare da wasu abubuwan da suka shafi abubuwan da aka tsara a kusa da shirin, in ji Uwargidan Erdogan.

Uwargidan shugaban kasar ta bayyana cewa, ana sa ran gudanar da taron kai tsaye na kwamitin ba da shawara na MDD karo na uku a COP29, kuma ta mika goron gayyata ga Guterres don ya halarta.

Da take yin la'akari da tashe-tashen hankula na baya-bayan nan, Emine Erdogan ta nuna alhininta game da barnar da yaƙe-yaƙe ke haifarwa, tana mai jaddada illar da ake yawan mantawa da ita ga yanayi da muhalli, wanda ke kara ta'azzara rikicin yanayi.

Bayan taron, UWargidan Erdogan ta wallafa a X, inda ta kira tattaunawarta da Guterres da "mai amfani" tare da jaddada aniyarsu ta kokarin kawar da bola a duniya.

TRT World